Jami’ar jihar Chicago a kasar Amurka, ta mayar da martani a kan bukatar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya gabatar wa da jami’ar, akan neman samun sahihanin shaidar karatun shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, da ya samu daga jami’ar.Â
A martanin jami’ar, ta nanata cewa, ba ta ajiye kwafin shaidar karatun da ta ke yaye dalibanta ba.
- Trump Ya Bayyana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Laifin Zamba
- Juyin Mulki: An Sake Bude Makarantu A Nijar Bayan Wata 3
Kazalika, jami’ar ta tabbatar da cewa, ta yaye shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, a shekarar 1979.
A cewar jami’ar, a shekarar 1979 ne ta yaye Tinubu wanda ya samu sakamakonsa na babban digiri a fannin karatun kasuwancin gudanar da mulki.
Bugu da kari, jami’ar ta bayyana cewa, bayan binciken da ta yi, ta samu wasu bayanai, amma ba za ta bayyana sunayen ba saboda matakan sirri.
Kazalika jami’ar ta bayyana cewa, ba ta iya samo abin da Atiku ya yi ikirari a kan cewar Tinubu ya bai wa hukumar zabe ta kasa INEC ba.
Sai dai, jami’ar ta sanar da cewa, ta gano takardar shaidar karatun difiloma kamar yadda Atiku ya gabatar da bukata ga jami’ar.