Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil a Jihar Kano, ta roƙi Gwamnatin Jihar da ta taimaka mata, bayan da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) ya katse ta daga cibiyar wutar lantarki ta ƙasa.
An dai katse wutar ne kimanin mako guda da ya gabata sakamakon bashin Naira miliyan ₦248m da kamfanin ya ke bin jami’ar. Bayan katse wutar jami’ar ta faɗa cikin duhu da kuma kawo cikas ga harkokin ilimi.
- Dan Takarar Majalisar Tarayya Na Mazabar Wudil Da Garko A Jam’iyyar NNPP Ya Rasu A Kano
- Rikicin Masarautar Kano: Kotu Ta Sake Ɗage Shari’ar Zuwa 4 Ga Watan Yuli
Shugaban harkokin ɗalibai Farfesa Abdulkadir Dambazau ya bayyana wa manema labarai irin halin da jami’ar ke ciki, inda ya bayyana cewa duk ƙoƙarin da aka yi na shawo kan KEDCO don dawo da wuta jami’ar bai yi nasara ba.
Duk da biyan Naira miliyan 20 daga cikin kuɗaɗen da ake bin jami’ar amma KEDCO ta dage kan ganin an daidaita wannan kudirin.
Farfesa Dambazau ya bayyana irin matsalolin da jami’ar ke fuskanta wajen ci gaba da gudanar da ayyukanta da suka haɗa da harkokin ilimi da samar da ruwan sha, ganin yawan ɗalibai da mutane kusan dubu ashirin da takwas ke cikin garari.
Ya bukaci gwamnatin jihar Kano da ta shiga tsakani tare da bayar da tallafin kuɗi domin magance matsalar.