Kamar yadda Mista Abayomi, yace jami’ar zata fara aiki ne ta amfani da sassa daban daban da suka shafi lamarin koyarwar kula da lafiya, inda asibitin koyarwa na jami’ar Legas zai kasance babban wurin da za a rika horo.
Kwamishinan lafiya na Jihar Legas,Akin Abayomi, yace kafa ita jami’ar harkar magunguna da sauarn lamurran da suka shafi kula da lafiya za su kara samar da kwararrun abinda ya shafi kiwon lafiya.
- Dalilin Da Ya Sa Legas, Abuja, Kaduna Suka Samu Masu Zuba Hannun Jari A Zango Na Uku
- Muhimman Dalilai 15 Na Tsara Yadda Malami Zai Koyar Da Darussa A Aji (3)
Da yake jawabi ranar Asabar a wajen bikin kaddamarwar a Legas Medipark Mista Abayomi yace idana bukatar maganin yadda kwararru suke ficewa zuwa kasashen waje (brain drain,) Shi cewa ya yi “ Muna samar da kwararrun ne (brain gain) ta jan hankalinsu yadda za su so zama su yi aiki domin Legas ta zama mai ban sha’awa ga mutane da yawa, za mu samar da kwararru kan bangaren magunguna da sauarn sassan kiwon lafiya cikin shekaru uku masu zuwa.”
Ya kara jaddada cewar “Ba da dadewa ba ne muka amince da daukar mataki na a kafa jami’ar lamurran magunguna da sauarn sassan kiwon lafiya,a traon mu na majalisara zartarwa,muna jiran amincewa majalisara Jihar Legas.”
Ya ce jami’ar za ta taimaka wajen samar da kwararru wadanda ta bangaren kula da lafiyar al’umma da suka hada da Likitoci, nas- nas, sauran kwararru na lamarin lafiya, masu hada magunguna, da Likitocin hakora,wanda suka cancanta su yi aiki a Medipark .
“Mun dauki matakan da suka kamata inda muna sa ran, nan da shekara biyar zuwa shida,za mu samar da kwararru 2,500 wadanda suka karanta al’amuran da suka shafi kula da laiyar al’umma, wadanda za su kasance sune ma’aikatan da ake bukata domin yin hakan.
Kara fadada jamai’ar harkar kula da lafiya
A watan Oktoba na wannan shekara majalisar zartarwa ta Jihar Legas ta amince da a kara fadada kwalejin koyon lamarin magunguna na jami’ar Jihar Legas,ta koma jami’ar koyon harkar magunguna ta Jihar Legas, zuwa jami’ar magunguna da da sauarn lamurran da suka shafi kiwon lafiya.
Kamar dai yadda Mista Abayomi ya yi karin haske, jami’ar za ta koyar da abubuwan da suka shafi kulawa da lafiyar al’umma tare da asibitin koyarwa na jami’ar Jihar Legas wanda zai kasance babban wurin da ake horarrwa.
Ya kara da cewa: “Babu gudu- babu- ja da baya dangane da maganar fadadawar wannan gwamnati ta riga ta dauri aniya. Mun samu wannan labari ne daga jaridar online ta Premium Times.