Babbar darektar ofishin Majalisar Dinkin Duniya (MDD) da ke Nairobi, babban birnin kasar Kenya, watau UNON, Zainab Hawa Bangura, ta bayyana cewa Bikin Bazara na al’ummar Sinawa na da matukar muhimmanci wajen samar da fahimtar juna da karfafa dankon zumunci a duniya.
Ta bayyana hakan ne yayin wani shagalin bikin al’adun Sinawa a kasar ta Kenya da ya gudana a jiya Laraba.
- Sin Ta Gabatar Da Karin Manufofin Gaggauta Bude Kofarta A Yankin Ciniki Cikin ’Yanci
- Shirin Tallafinmu Ga Nijeriya A 2025 Zai Kai Ga Asalin Mabukata – Wakilin MDD
Bikin wanda aka gudanar a harabar UNON, ya baje kolin al’adu, da suka hada da wasannin tale jiki da tsalle-tsalle, da abincin Sinawa, da nune-nunen tufafin ado da zane-zane na gargajiya.
Bikin na rabin yini wanda UNON da ofishin jakadancin kasar Sin da ke Kenya da kuma babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin (CMG) suka dauki nauyin shiryawa, ya samu halartar manyan jami’an gwamnatin kasar, da jami’an diflomasiyya, da malamai da daliban jami’o’i, inda suka nuna farin ciki da bikin wanda ya karfafa cudanya a tsakanin al’adu.
Bangura ta kuma bayyana cewa, bikin bazara, wanda Kungiyar Kula da Ilimi da Kimiya da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) ta aminta da shi a hukumance, a ranar 4 ga watan Disamba, 2024, tare da sanya shi cikin jerin manyan al’adun bil’adama na bukukuwa, ya zama wata babbar alama ta al’adun Sinawa, da ke kara karfafa cudanya a tsakanin al’adu da wayewar kan duniya mabambanta.
Jami’ar ta MDD ta kuma jaddada muhimmancin rawar da cibiyoyin da suka kunshi al’ummomi daban-daban ke takawa wajen hada kan jama’a don gudanar da shagulgulan ire-iren wadannan bukukuwan, wadanda suke samar da daidaito da hadin gwiwa a duk duniya.
Ta kuma ta’allaka jigogin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya da ke kunshe a cikin bikin bazara da babban manufar MDD ta karfafa hadin kai da zaman tare mai dorewa a duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp