Daraktan ofishin kula da harkokin wajen kasar Sin na kwamitin kolin JKS Wang Yi, ya gana da ministan harkokin wajen Gabon Hermann Immongault, yau Litinin a birnin Beijing.
Da yake bayyana aminci a siyasance dake tsakanin Sin da Gabon a matsayin muhimmiyar fa’idar dangantakarsu, Wang Yi ya ce a shirye Sin take su ci gaba da goyon bayan juna wajen kare muradunsu da inganta hadin gwiwa a karin fannoni da manyan matakai da kuma hada hannu wajen daukaka ka’idojin huldar kasa da kasa.
A nasa bangare, Hermann Immongault, ya ce Gabon na yabawa gudunmuwar da Sin ke bayarwa ga zaman lafiya da ci gaban duniya, haka kuma tana godiya da jerin shirye-shiryen hadin gwiwa da Sin ke gabatarwa kan hadin gwiwarta da Afrika. A cewarsa, a shirye Gabon take ta hada hannu da Sin wajen inganta gina al’umma mai makoma ta bai daya ta Sin da Afrika. (Fa’iza)