Kasar Kenya na amfani da damar ci gaban fasahar kasar Sin don kara dogaro da samar da wutar lantarki a kasar.
Darektan ma’aikatar kula da harkokin rarraba wutar lantarki ta kasar Joseph Siror ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, inda ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Nairobi, babban birnin kasar Kenya cewa, ababen more rayuwa a fannin samar da wutar lantakin kasar na kunshe da dimbin kayayyakin aiki daga kamfanonin kasar Sin irin su Huawei da rukunin Yocean.
- An Kammala Aikin Tsugunar Da Mutane A Gundumar Tingri Ta Sin Bayan Bala’in Girgizar Kasa
- Ƴansanda Za Su Fara Tilasta Yin Insuran Motoci Daga 1 Ga Fabrairu
“Sashen wutar lantarki na Kenya ya kuma ci moriyar musayar fasaha da kara sanin makamar aiki daga kamfanonin kasar Sin,” kamar yadda Siror ya bayyana a lokacin da kamfanin ya fitar da sakamakon rabin shekarar da ta gabata a ranar 31 ga Disamban 2024.
Siror ya kara cewa, masana’antun kasar Sin da dama sun yi nasara a takarar neman samar wa ma’aikatar wutar lantarki ta Kenya da na’urorin wutar lantarki saboda ci gaban fasaharsu da kuma karfi a bangaren hada-hadar kudi. Ya jaddada cewa, ta hanyar hadin gwiwa da kamfanonin kasar Sin, kasar Kenya ta samu damar samun hanyoyin samun kayayyakin wutar lantarki masu inganci kuma na zamani, da tsarin rarraba makamashi mai inganci, da na’urorin tantance yawan amfani da lantarki na zamani. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)