An bayyana taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika (FOCAC) da aka shirya gudanarwa a watan Satumban bana, a matsayin wanda zai karawa dangantakar Sin da Kenya da ta shafe sama da shekaru 60 kuzari.
Sakataren gwamnatin kasar Kenya mai kula da harkokin kasashen waje, Musalia Mudavadi ne ya bayyana haka a jiya Talata, yayin ganawarsa da wakilan al’ummar Sinawa a Nairobi, babban birnin kasar. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)