Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake ‘yan Nijeriya da su kara yi wa gwamnatinsa hakuri, inda ya ce sauki na nan tafe.
Shugaban ya sake yin jawabi ne ga ‘yan Najeriya a wani sabon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X (twitter) a ranar Laraba.
- Nijeriya Na Kashe Dala Miliyan 600 Wajen Shigo Da Mai Duk Wata – Minista
- Tinubu Ya Binciki Kuɗaɗen Da Yake Bai Wa Gwamnoni – Sheikh Yakubu Musa
Wannan na zuwa ne bayan jawabin farko da ya yi a ranar Lahadin da ta gabata sakamakon zanga-zangar tsadar rayuwa da kuma adawa da matakansa na tattalin arziki.
A cikin jawabinsa, Tinubu ya jadadda cewa yana sane da halin kuncin rayuwa da ‘yan Nijeriya suka shiga sakamakon janye tallafin fetur.
‘Yan Nijeriya da dama ne suka gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa, inda wasunsu da dama ke kira ga shugaban ya dawo da tallafin man fetur da ya cire.
Amma a sabon jawabinsa, shugaban ya ce yana sane da wahalar da ‘an Nujeriya ke ciki tare da nanata cewa wahala ce ta dan kankanin lokaci.
Amma zanga-zangar da aka yi ta haifar da tashe-tashen hankula a wasu yankuna na Nijeriya, ciki har da salwantar rayukan ‘yan kasar.