Jam’iyyar APC ta lashe kujerun ‘ya majalisun dokokin jihar Kaduna na mazaɓar Zariya da Kewaye da Basawa da aka gudanar a ranar Asabar 16 ga watan Agusta, 2025.
Da yake bayyana sakamakon zaɓen mazaɓar Zariya da Kewaye a safiyar Lahadi, jami’in hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) Farfesa Balarabe Abdullahi ya ce dan takarar jam’iyyar APC, Isa Haruna Ihamo ya samu kuri’u 26,613.
- UNICEF Ya Jaddada Muhimmancin Yi Wa Yaran Afirka Rajistar Haihuwa
- Kasashen Sahel Na Bukatar Agaji Domin Yaki Ta’addanci -Rasha
Sai Kuma dan takarar jam’iyyar (SDP), Nuhu Sada Abdullahi ya samu kuri’u 5,721, yayin da dan takarar (PDP), Mamuda Abdullahi Wappa ya samu kuri’u 5,331.
Hakazalika, da yake bayyana sakamakon karshe na zaben cike gurbi na mazabar Basawa, Farfesa Nasiru Rabi’u ya bayyana dan takarar jam’iyyar APC a matsayin Wanda ya lashe zaben.
A cewarsa, APC ta samu kuri’u 10,926, yayin da jam’iyyar PDP ta samu 5,499.
Zabukan wadanda aka gudanar dasu cikin tsauraron matakan tsaro, an kammala Su cikin lumana duk da cewa an samu matsalar rashin fitowar jama’a yadda ya kamata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp