Jam’iyyar NNPP a Jihar Kaduna ta ƙaryata rahoton da ake yaɗawa cewa an tsige shugaban jam’iyyar na jihar, Alhaji Mohammed Lawal Sultan, wanda wasu da aka kora daga jam’iyyar suka sanar.
Shugabancin jam’iyyar ya bayyana cewa, waɗanda suka yi wannan sanarwar na ƙarya an kore su daga jam’iyyar tun da daɗewa bisa ayyukan da suka saɓa wa jam’iyya da kuma haɗa kai da ‘yan adawa domin yi wa jam’iyyar zagon ƙasa.
- An Ɗage Shari’ar Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Zuwa 19 Ga Watan Nuwamba
- Kwankwaso Ya Gana Da Shugabannin NNPP A Kuros Ribas Don Tunkarar Zaɓen 2027
A cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar NNPP na Jihar Kaduna, Alhaji Zubairu Mai Anguwa, ya fitar, ya ce waɗanda suka ɗauki nauyin wannan sanarwa ba su kasance mambobin jam’iyyar ba tsawon lokaci.
Ya ce shugabancin jam’iyyar ya shigar da ƙorafi ga ‘yansanda da kuma hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) kan abin da ya kira sojan gona da kuma ƙarya ta iƙirarin zama mambobin jam’iyyar da wasu mutane biyu da suka haɗa da Jumare Tanimu Magaji da Joshua Madaki.
“Ina so in fayyace cewa waɗannan mutanen da suka ce sun tsige shugaban, an kore su daga jam’iyyar tun da daɗewa saboda ayyukan da suka saɓa wa jam’iyya da kuma haɗa kai da ‘yan adawa domin su haifar da rikici a cikin NNPP,” in ji shi.
Ya tabbatar da cewa jam’iyyar NNPP a Kaduna tana cikin haɗin kai da zaman lafiya, inda ya bayyana batun tsige shugaban a matsayin yunƙurin ƙirƙirar rikici da tashin hankali a cikin jam’iyyar.













