Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano ta bukaci hukumomin tsaro da su samar da zaman lafiya ba tare da tashin hankali ba a ranar 11 ga Maris a jihar.
Wani jigo a jam’iyyar Dokta Bappa Bichi ne ya yi wannan roko a ranar Litinin a wani taron manema labarai a Kano.
- Wike Ya Yi Wa Atiku Shagube Kan Zanga-Zangar Neman INEC Ta Soke Zaben Shugaban Kasa
- Kasar Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Bunkasa Tattalin Arzikin Duniya
Bichi ya ce sha’awar ‘yan Nijeriya na zaben shugabannin da suke so ba zai yiwu ba idan hukumomin tsaro suka gaza samar da daidaito ga dukkanin jam’iyyun siyasa.
A cewarsa, hakan zai ba da damar gudanar da zabe na gaskiya da adalci.
Ya kuma bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da hukumomin tsaro da su kasance ‘yan ba ruwana kuma masu gaskiya da kuma rashin nuna bangaranci wajen gudanar da ayyukansu a lokacin da kuma bayan kammala aikin.
A cewarsa, jam’iyyar NNPP jam’iyya ce mai son zaman lafiya kuma tana gudanar da ayyukanta ba tare da wani tashin hankali na siyasa da ‘yan daba ba.
“Bari na yi amfani da wannan dama wajen tabbatar da cewa jam’iyyarmu ta NNPP ba za ta iya ba kuma ba za ta taba mika wuya ga tsoratarwa ko barazana ga kowa ba.
“Ba za mu zauna a banza muna kallon yadda ake cin zarafi da cin mutuncin mambobinmu ba, da tsoratarwa daga gwamnati ba tare da wani dalili ba,” in ji jigon jam’iyyar.
A cewarsa, akwai bukatar gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa an samar da fili daidai gwargwado ga duk masu ruwa da tsaki da suka cancanta domin shiga zaben ba tare da barazana ga rayuka da dukiyoyi ba.
“Ba za mu taba bari a sace muradin mutane ba. Sun kwace mana iko a 2019. Mun hana magoya bayanmu tare da hana su fitowa kan tituna suna zanga-zangar.
Ya yi gargadin “A wannan karon zai yi wahala mu bari sake takurawa magoya bayanmu.”