Jam’iyyar PDP reshen jihar Kebbi ta bayyana cewa ta shirya tsaf domin tarbar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, GCON, a ranar 12 ga watan Nuwamba a jihar.
Da yake jawabi ga manema labarai a Birnin Kebbi, babban birnin jihar, Barista Kabiru Tanimu Turaki SAN, mamba a kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP (BOT) ya ce makasudin taron nasu shi ne duba shirye-shiryen karbar dan takararsu na shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar.
Barista Kabiru Turaki, wanda tsohon ministan ayyuka na musamman ne, ya ce makasudin taron shi ne duba shirye-shiryen karbar dan takararsu na shugaban kasa.
Ya ce: “Abin da za a yi a yau shi ne duba shirye-shiryen karbar dan takararmu na shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, GCON, Wazirin Adamawa, wanda ake sa ran zai ziyarce mu a nan Kebbi a ranar Asabar 12 ga watan Nuwamba, 2022 don gudanar da yakin neman zaben shugaban kasa ga al’ummar jihar.
Haka kuma, Barista Turaki ya tunatar da cewa ziyarar da Atiku ya kai jihar Kebbi a shekarar 2019 ita ce mafi kyau da aka taba samu a kasar nan, yayin da ya kuma ba da tabbacin jam’iyyar ta kuduri aniyar yiwa maziyartan liyafar da ta dace fiye da ziyarar da ya kawo a baya.
“Don haka kudurinmu a yau shi ne mu ma mu rubanya adadin mutane, mun zauna mun kafa kwamitocin da za su yi aiki awa 24 daga yanzu har zuwan sa da kuma tafiyarsa a ranakun 12 da 13 ga Nuwamba, 2022.
“Daga nan za mu ziyarci filin wasa na Birnin Kebbi domin duba irin ayyukan da ake yi a can.
“Don haka muna so mu tabbatar wa ‘yan Nijeriya da mambobin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa cewa shugabancin jam’iyyar PDP a jihar Kebbi a shirye yake ya karbi dan takararta na shugaban kasa,, a Jihar kebbi, in ji shi”.
Daga karshe, Barista Kabiru Turaki SAN, ya lissafa kwamitocin da suka hada da; babban kwamitin da tsohon Janar Ishaya Bamaiyi zai jagoranta, kwamitin wurin, kwamitin tsaro, kwamitin masauki, kwamitin sufuri, kwamitin nishaɗi da kwamitin yada labarai.