Jam’iyyar Zenith Labour Party ZLP ta tsayar da ‘yan takara a dukkan matakai don tunkarar shiga zaben 2023, dan takarar Gwamnan Jihar Kano a karkashin jam’iyyar, Alhaji Isah Nuhu Isah ya bayyana haka bayan tabbatar da shi a matsayin.
Ya ce, suna da kyakkyawan manufa da kudurori da in Allah ya amince mutane suka zabesu za su tabbatar ba su yi zaben tumun dare ba. Don za su bada kulawa ga Ilimi da lafiya da samar da aiki ga matasa maza da mata.
Ya yi nuni da cewa, cin zabe da rashinsa Allah ne, kuma ba wata babbar jam’iyya da za ta tsorata su a shiga zabe don haka ya ja hankalin mutane a kan a daina tsorata su da cewa sai mai babbar jam’iyya ko mai babbar riga ko mai dogon zurfin ilimi ne zai samu mulki. Abinda akeso a neman mulki shi ne wanda yake da gaskiya da amana da kyakkyawan mu’amala da mutane shi yakamata a zaba. Kuma Jama’a shaida ne a kansa sun san wanene shi.
Ya ce ba wata jam’iyya da tafi wata Allah shi yake bada mulki kamar yanda ya baiwa Gwamnan Zamfara. Duk wanda yaga sun yi masa da kira ga sauran dukkan jama”a su tabbatar sun mara wa jam’iyyar ZLP baya ta kafa Gwamnati a Kano saboda a yanzu haka ma sunada yan takara na majslisun jahar dana tarayya dana Sanatoci Uku da shi da yake takarar Gwamna.