• English
  • Business News
Monday, November 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jan Yara A Jiki Ba Tare Da Duka Ko Zagi Ba Ne Sirrin Nasarar Koyarwa—Saratu Magaji Jahun

by Bushira Nakura
3 years ago
Zagi

Saratu Magaji Usman Jahun Malamar makaranta ce wadda ta riki sana’ar koyarwar da hannu biyu-biyu, a tattunawarsu da Wakiliyarmu Bushira Nakura, ta bayyana yadda ta tsinci kanta a fagen koyarwa ta kuma yi bayanin wasu sirrorin da ke tattare da sana’ar, ta kuma yi tsokaci a kan tarihin rayuwarta. Ga dai yadda tattaunawarsu ta kasance:

Da farko masu karatu za su so su ji cikakken sunanki da kuma sunan da aka fi saninki da shi, tare da dan takaitaccen tarihinki.

Dafar ko dai sunana Saratu Magaji Usman Jahun anfi sanina da Saratu Magaji Jahun, an haife ni a garin Jahun cikin karamar hukumar Jahun ta Jihar Jigawa, na yi karatun Firamare a Jahun, na yi Sakandire makarantar ‘yan mata ta Arabic Kaugama, na kai matakin NCE daga nan na yi aure na hayayyafa don ina da yara guda bakwai, ina jin dadin zaman aurena, Allah ya kara mana zaman lafiya mai dorewa.

Me ya ja hankalinki ko me ya baki sha’awa har kika zabi harkar koyarwa?

Alhamdulillah koyar wa abune mai kyau a cikin al-umma ina da ra’ayin  koyarwa tun ina kuruciya kuma har girma ya zo na tsinci kaina a harka ta koyarwa na yi farin ciki da kasan cewata malama sosai domin abin dama yana raina, Allah ya saka wa Malam mu da alkhairi,  Allah ya kara mana basira da hazaka.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu

Tsokaci A Kan Mata Masu Tsananin Kishi

Ya farkon fara koyarwar ki ta kasance wace hanya kike bi wajen shawo kan dalibanki

Kuma wacce hanya kike bi kuma ya kika tsinci kanki lokacin da kika shiga aji kasan cewar wasu na son yi amma suna jin tsoro ko kunya ke ma kin fuskanci kanki a irin wannan matsalar ko kuwa?

Da farko shiga ta aji na ji kunya gaskiya amma a hankali a hankali na saba sosai duba da irin shawarwarin da abokan aiki na suke bani  ba zan manta da Malama Halima Mukthar Jahun ba ta bani kwarin gwiywa matuka gaya Allah ya saka mata da alkhairi, sannu a hankali har na goge, na kan shiga aji zuciya ta tsab na yi koyarwata hankali kwance ina jin dadin koyarwa alal hakika gaskiya Allah ya kara mana baiwar koyar wa da hazakar shiga aji.  Na kan ji sanyi har cikin zuciya ta yayin da na shiga aji na ji yara na fadin” Malama Malama kece a jin mu” na kan yi dariya ka shiga ajin ina son dalibaina na shekarar 2004 suma suna sona sosai.

Daga lokacin da kika fara koyarwa zuwa iyanzu za ki kai kamar shekara nawa kina yi?

Na kai shekara goma sha tara ina koyarwa daga farawata zuwa yanzu da na dan samu dan canje-canje na wajen aiki.

Taya kike iya hada harkokin Gida da Aiki Masalam kula da yara kula da maigida tsaftar gida abinci da sauransu?

Wannan shi ne abu me sauki, domin tunda nasan zan fita aiki, to ya zama wajibi na tsara  fita aikina da kuma aikace aikacen gida. Ina  fara rage wasu ayyukan gidan kafin na fita, zancen Maigida da yara kuma mukam fita gaba daya sannan kusan tare muke dawowa.

Ya kike ganin yadda karbuwar ki a daga yaran da kike koyarwa?

Ita koyarwa abune da ke son jan yara a jiki, ba tare da duka ko zagi ba, Yaba wa yara lokacin da suka yi abu koda kuskure ne, daga baya sai a sanar dasu cewa hakan ba daidai ba ne, kaza ne daidai. Yara suna aso hakan.

Ta wacce hanya kike bi wajen ganin kin tankwara yaran wajen bin abinda kike so su yi?

Nakan yi abinda suke so, nima sukan yi abin da nake so.

Kowa ya san koyarwa na da wahala matuka musamman ma ta kanana yara ko me zaki ce a kan wannan?

In har ka fahimci yaran, koyar dasu ba zai ma mutum wahala ba kamar dai yadda nace jansu a jiki shi ne kaso mafi girma da malamai za su yi.

Wanne irin kalubale kika taba fuskanta ga yaran ko iyayensu ko makamancin haka, me za ki ce a kan hakan?

Gaskiya ne ko wanne abu ya same ka a rayuwa sai da kalubale amma alhamdulillah ban samu kalube a cikin koyarwa da zai dameni ba saboda ‘yar kiyayya ce ta bangaren yara ai dole kasame ta duba da yanayin zamantakewa.

Wadanne irin nasarorin kika samu game da wannan sana’an naki?

Nasara Alhamdulillah, wallahi munsameta sai fatan alkhairi ba abinda zamu cewa Allah, sai godiya da fatan ya kara mana daukaka.

Shin kin taba yi a ran ki cewar dama baki zabi wannan layin na koyarwa ba ko kuwa?

Ban taba jin cewa dama ban zama Malamar makaranta ba saboda ina son koyarwa yana bani sha’awa arayuwa ta ina so na kasance Malam ta har abada Alhamdulillah.

Mene ne burinki na gaba game da wannan sana’aki?

Tofa, burina bai wucena zama shugabar makaranta (principal) ba.

Kamar wanne abu ne ya taba faruwa da ke na farin ciki ko akasin haka wanda ba za ki taba mantawa da shi ba?

Ranar da na fara karbar albashi na dubu bawai da dari duhu, na yi farin ciki ba kadan ba wallahi na yi murna na gode wa Allah subuhanahu wataala da ni’imar da ya yi min Alhamdulillah ala kullu halin.

Daga lokacin da kika fara koyar wa kawo yanzu zaki kai kamar shekara nawa?

Na kai shekara goma sha tara ina koyarwa daga farawata zuwa yanzu duk da  na dan samu dan canje-canjen a wajen aiki .

Idan kina wata sana’ar ya tsarin kasuwancin yake kasancewa, kuma ya bambancin yake kamar wajen yadda sana’ar take kawo kudi da sauransu?

Ba laifi Alhamdulillah,  sana’a tana kawo kudi, musamman idan wata ya yi nisa, ko kuma kan samu wasu suna riga wasu albashi, kinga in kana sana’a zaki samu wanda za su biyaki, kafin a samu albashi.

Wanne kira za ki yi ga matasa musamman mata wadanda ba sa sana’a ba su da abin yi, har ma da manya na gida, me za ki ce akansu?

Hakika zama ba zai yiwu babu aikinyi ba ko  kuma sana’a ba, rayuwa yanzun dole sai da neman na kai, komai kankantar sa  kuwa.

Mace da zaki gane cewa Itafa sana’a girma da daraja take karawa mutum a ko ina walau gidanki, gidanku, abokanki da duk wanda kuke tare dasu. Ya ke ‘yar uwa ki daure ki koyi sana’a kodan rufawa kanki da yaranki da iyayen ki asiri, saboda idan baki dashi ma bame nemanki.

Ko akwai wani kira da za ki ga gwamnati game da masu kokarin yin sana’a?

Mukam anan Jigawa Gwamnati na baki kokarinta a wajen bama mata jari, domin su dogara da kansu.To Alhamdulillah.

Me za ki ce da wannan shafi na Adon Gari?

Ba abunda zance wa adon gari Daya wuce fatan kara samun nasara da daukaka a fannin aikin su Allah ya kara musu farin jini a idanun Al-umma.

Me za ki ce da Jaridar Leadership Hausa?

Allah ya kara muku dunbum masoya ku yi suna sosai ta fannin aikin ku a idon duniya Ya sa ku zamo lamba na daya a duniya.

Ko kina da wadanda za ki gaisar?

Sosai kuwa abokan kuruciya da abokan zaman duniya na yau da kullum ina gaida iyalaina da ‘yan uwana fantan alkhairi ga abokan rayuwa ta na yau da gobe sun san kansu, ina gaida Bushira Aminu Nakura kawata Aminiyata Abokiyar shawarata

Na gode sosai.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu
Taskira

Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu

October 19, 2025
Kishi
Taskira

Tsokaci A Kan Mata Masu Tsananin Kishi

October 12, 2025
Illolin Da Ke Tattare Da Mallaka Wa Kananan Yara Wayar Hannu
Taskira

Illolin Da Ke Tattare Da Mallaka Wa Kananan Yara Wayar Hannu

October 4, 2025
Next Post
Kasar Sin: An Yi Tafiye-tafiye Sama Da Miliyan 300 A Lokacin Hutun Bikin Bazara 

Kasar Sin: An Yi Tafiye-tafiye Sama Da Miliyan 300 A Lokacin Hutun Bikin Bazara 

LABARAI MASU NASABA

Kano

Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi

November 3, 2025
Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

November 2, 2025
Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

November 2, 2025
Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

November 2, 2025
Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

November 2, 2025
Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

November 2, 2025
Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

November 2, 2025
Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

November 2, 2025
Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

November 2, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su

November 2, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.