Rahotanni daga manema labarai na kafar CMG ta kasar Sin, na cewa jarin da ake zubawa a fannin bincike, da samar da ci gaban manyan kamfanoni mallakar gwamnatin kasar Sin, ya haura yuan tiriliyan daya cikin shekaru 2 a jere.
An fitar da bayanan hakan ne yayin dandali na 7, na kamfanonin kasar Sin, wanda ya gudana a baya bayan nan a birnin Beijing. Yayin gudanar da dandalin, hukumar jagoranci da sanya ido kan kadarori mallakin gwamnatin tsakiyar kasar Sin, wadda ke karkashin majalissar gudanarwa ta Sin, ta fitar da rahoto mai taken “Rahoto game da ci gaba mai inganci na manyan kamfanonin gwamnati na shekarar 2024,” wanda ya yi bayani dalla-dalla game da sabbin nasarori da manyan kamfanoni mallakar gwamnatin kasar Sin suka cimma a shekarun baya bayan nan.
- Me Ya Sa Kasar Sin Ta Shirya Bikin CIIE?
- Tinubu Zai Halarci Taron Haɗin Gwiwar Larabawa Da Musulmai A Saudiya
Game da hakan, mataimakin darakta a hukumar Tan Zuojun, ya ce a bara, jarin da aka zuba a sassan sabbin masana’antu masu matukar fa’ida, ya karu da kaso 32.1% a shekara, yayin da ribar da suka samar ta haura yuan tiriliyan 10.
Kaza lika, tsakanin watan Janairu da Satumban bana, jarin da aka zuba a fannin ya karu da kaso 17.6% a shekara, wanda ya kai kusa kaso 40% na jimillar jarin da aka zuba a daukacin kamfanoni mallakin gwamnatin tsakiyar kasar, wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen ingiza samar da hajoji masu nagarta.
Tan Zuojun, ya kara da cewa, a nan gaba hukumarsa za ta mayar da hankali ga bunkasa manufofin samar da sabbin hajoji masu inganci, da ingiza bunkasar masana’antu, da amfani da ci gaban kimiyya da fasaha. Har ila yau, za a aiwatar da matakan ingiza kirkire-kirkire, da cimma gajiyar basira, da bullo da sabbin masana’antu, da sabbin dabarun samar da ci gaban su. (mai fassara: Saminu)