Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta ce jarin kai tsaye na waje da ba na kudi ba da Sin ta zuba a ketare, cikin watanni 8 na farkon shekarar nan ya kai dala biliyan 94.09, karuwar da ta kai ta kaso 12.4 bisa dari a shekara.
Yayin taron manema labarai na Alhamis din nan, wanda ma’aikatar ta gudanar, ta gabatar da alkaluman jarin waje na Sin da hadin gwiwa da sauran sassan ketare tsakanin watannin Janairu zuwa Agusta.
A cikin adadin, kamfanonin kasar Sin sun zuba jarin dalar Amurka biliyan 20.51 a fannonin jarin kai tsaye da ba na hada hadar kudi ba, a kasashen da suka shiga shawarar ziri daya da hanya daya, wanda hakan ya nuna karuwar kaso 2.2 bisa dari na adadin a shekara. (Mai fassara: Saminu Alhassan)