Wani ɗan Fashi da makami ya rasa ransa bayan da yayi yunƙurin yin fashi a unguwar Dorayi Babba, Unguwar Jakada, Kano. Rahotanni sun bayyana cewa ɓarawon, wanda aka gano sunansa Musa Nuhu, ya kutsa cikin wani gida riƙe da makami, wata wuka da nufin yin fashi a wani gida.
Bayan shiga cikin gidan, ɓarawon ya kai hari kan wasu mata biyu tare da jikkata su. Sai dai wani namiji daga cikin iyalan gidan yai taho mu gama da ɓarawon a cikin wata fafatawa mai zafi da ta jawo raunika a tsakaninsu duka biyu.
- Gwamna Yusuf Ya Jagoranci Tawagar Kano Zuwa Jana’izar Marigayi Aminu Dantata A Madina
- An Sauya Sunan Makarantar Wasanni Don Girmama Ƴan Kano Da Suka Yi Hatsari
Kakakin rundunar Ƴansanda ta Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa a shafinsa na Facebook. Ya bayyana cewa an yi nasarar daƙile harin ne sakamakon jarumtar da ɗaya daga cikin mazauna gidan ya nuna.
“An sami nasarar daƙile ɓarawon bayan wata fafatawa da wanda ake yunƙurin kai wa hari ya yi. An garzaya da shi asibiti domin samun kulawa, amma daga baya likitoci suka tabbatar da mutuwarsa sakamakon munanan raunukan da ya samu,”
in ji sanarwar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp