ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, November 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jarumin Nollywood, Pete Edochie, Ya Rasu Yana Da Shekara 79

by Sadiq
51 seconds ago

Fitaccen jarumin fina-finan Nijeriya, Pete Edochie, ya rasu yana da shekara 79 a duniya.

Marigayin ya rasu ne da misalin ƙarfe 12:30 na daren ranar Laraba, 25 ga watan Nuwamba, 2026, a birnin Enugu da ke Nijeriya, bayan fama da rashin lafiya.

Ɗansa, Leo Pete Edochie ne, ya sanar da rasuwar mahaifinsa a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Instagram a madadin iyalansa.

ADVERTISEMENT

A cikin sanarwar, iyalan marigayin sun bayyana alhininsu kan rasuwar jarumin, tare da bayyana shi a matsayin uba, miji, ɗan uwa kuma jigo a cikin iyalansu.

Pete Edochie, ya taka rawa a fina-finan Nollywood, ya yi fice sosai bayan fitowarsa a matsayin Okonkwo a cikin fim ɗin talabijin na Things Fall Apart, wanda aka shirya daga littafin marubucin Nijeriya, Chinua Achebe.

LABARAI MASU NASABA

Bayan Dakatar Da Sarkin Daura, Gwamnatin Katsina Ta Kafa Kwamitin Bincike

Majalisa Ta Amince Da Shirin Tinubu Na Karɓar Bashin Dala Biliyan 20.5 Da Yuro Biliyan 1.45

An haifi jarumin ne a ranar 7 ga watan Maris, 1947, garin a Zariya, Jihar Kaduna, amma asalinsa daga Akamnato, Ifite Nteje, da ke Jihar Anambra.

Kafin ya shahara a harkar fim, Edochie ya yi aikin watsa labarai, inda ya fara aiki a matsayin mai gabatar da shirye-shirye a shekarar 1967.

A tsawon rayuwarsa, ya taka rawa a fina-finai da dama, inda ya samu karɓuwa a Nijeriya da sauran sassan duniya saboda ƙwarewarsa, musamman yadda yake taka rawar dattijo da masu mulki.

Gwamnatin Nijeriya ta karrama shi da lambar yabo ta ƙasa ta Member of the Order of the Niger (MON) saboda gudunmawar da ya bayar ga ƙasar.

Marigayin ya rasu ya bar matarsa, Josephine Edochie, ’ya’yansa da sauran ’yan uwa.

Iyalansa sun ce za su sanar da shirye-shiryen jana’izarsa nan gaba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Bayan Dakatar Da Sarkin Daura, Gwamnatin Katsina Ta Kafa Kwamitin Bincike
Manyan Labarai

Bayan Dakatar Da Sarkin Daura, Gwamnatin Katsina Ta Kafa Kwamitin Bincike

November 24, 2026
Sabbin Ministoci
Manyan Labarai

Majalisa Ta Amince Da Shirin Tinubu Na Karɓar Bashin Dala Biliyan 20.5 Da Yuro Biliyan 1.45

November 24, 2026
Senegal Ce Ta Lashe Kofin Afrika na 2025 – Kotu
Manyan Labarai

Senegal Ce Ta Lashe Kofin Afrika na 2025 – Kotu

November 24, 2026

LABARAI MASU NASABA

Jarumin Nollywood, Pete Edochie, Ya Rasu Yana Da Shekara 79

Jarumin Nollywood, Pete Edochie, Ya Rasu Yana Da Shekara 79

November 25, 2026
CGTN Ta Gudanar Da Taron Tattaunawa Kan Nazarin Darussan JKS A Kasashe Masu Tasowa Da Dama

CGTN Ta Gudanar Da Taron Tattaunawa Kan Nazarin Darussan JKS A Kasashe Masu Tasowa Da Dama

November 24, 2026
Sin Ta Tsawaita Waadin Dakatar Da Fitar Da Kayayyakin Da Ake Amfani Da Su A Aikin Soji Da Na Farar Hula Zuwa Amurka

Sin Ta Tsawaita Waadin Dakatar Da Fitar Da Kayayyakin Da Ake Amfani Da Su A Aikin Soji Da Na Farar Hula Zuwa Amurka

November 24, 2026
Gwamnatin Kaduna Ta Jajantawa Mahukunta Gidan Rediyon Tarayya  Kaduna Bisa Ifti’lain Gobara

Gwamnatin Kaduna Ta Jajantawa Mahukunta Gidan Rediyon Tarayya Kaduna Bisa Ifti’lain Gobara

November 24, 2026
Sin Ta Mai Da Martani Kan Sabuwar Yarjejeniya Tsakanin Tsibiran Solomon Da Austriliya

Sin Ta Mai Da Martani Kan Sabuwar Yarjejeniya Tsakanin Tsibiran Solomon Da Austriliya

November 24, 2026
Auren Gata: Za A Saka Wa Kowace Amarya Kuɗin Sadakinta N200,000 A Asusunta

Kwankwasiyya Ta Ƙalubalanci Gwamna Abba Ya Kawo Hujja Kan Zargin Yarjejeniyar Komawa APC

November 24, 2026
Sin Na Cikin Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Neman Izinin Mallakar Fasahar 6G

Sin Na Cikin Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Neman Izinin Mallakar Fasahar 6G

November 24, 2026
An Kashe Makiyaya Biyu a Wani Sabon Hari a Filato

’Yan Bindiga Sun Kashe Matasa Biyu, Sun Sace Shanu 150 A Filato

November 24, 2026
Jami’an Sin Da AU Sun Tattauna Kan Tsare-tsaren Gargadin Wuri Game Da Yanayi

Jami’an Sin Da AU Sun Tattauna Kan Tsare-tsaren Gargadin Wuri Game Da Yanayi

November 24, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ya Karrama Direbobi 35 Masu Ƙwazo

Kamfanin Simintin Dangote Ya Karrama Direbobi 35 Masu Ƙwazo

November 24, 2026

© 2026 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2026 Leadership Media Group - All Right Reserved.