‘Yan uwana ‘yan Nijeriya, Ina farin cikin gabatar muku da jawabi a yau, ranar cikar kasarmu shekaru 63 da samun ‘yancin kai, a matsayina na shugaban kasarmu mai albarka kuma dan uwanku dan Nijeriya.
2. A wannan rana mai muhimmanci mai cike da fatan alheri, muna jinjina ga iyayenmu da suka kafa Nijeriya mazansu da matansu. Ba don su ba, da ba a samu kasar Nijeriya ba. Gwagwarmayarsu da sadaukarwarsu da jagorancinsu ne suka haifar da ‘yantacciyar kasar Nijeriya mai mulkin kanta.
- Tinubu Ya Jaddada Aniyar Magance Rashin Tsaro Da Talauci A Nijeriya
- Tinubu Ya Umarci A Gaggauta Ceto Matan Jami’ar Gusau Da Aka Yi Garkuwa Da Su
3. A wannan lokacin, muna karfafa wa juna gwiwar cewa a matsayinmu na ‘yan Nijeriya, Allah ya yi mana baiwa a dunkule da kuma a daidaikunmu. Babu wanda ya fi wani a cikinmu. Nasarorin da Nijeriya ta cimma su ne abin alfaharinmu. Kalubalen da muka jure wa su ne ke karfafarmu. Kuma babu wata kasa ko wani iko a duniya da zai iya dankwafe mu daga isa matsayin da ya dace da mu. Wannan kasar taku ce, ‘yan uwana. Ku so ta, ku karrama ta a matsayinta ta kasarku ta kanku.
4. Nijeriya ta isa kasa a bar misali bisa yanayin zubi da tsarinta. Allah ya azurta mu da kabilu, addinai, da al’adu daban-daban. Sai dai dankon zumuncin da ke tsakaninmu ya na da matukar karfi ko da yake ba ganinsa ake ba. Mun hadu kan buri guda daya na samar da zaman lafiya da ci gaban al’umma, da fata guda na bunkasar arziki da hadin kai da kuma manufofin hadaka na juriya da adalci.
5. Samar da kasa da aka dora bisa harsashin aiwatar da wadannan manufofi masu daraja kan al’ummomi mabanbata ya zamo aiki mai matukar albarka da yake fama da kalubale. Wadansu mutanen sun ce bai kamata a samu ‘yantacciyar kasar Nijeriya ba. Wasu sun ce kasarmu za ta rushe. Har abada su na kan kuskure. A nan kasarmu ta kafu kuma a nan za ta tabbata.
6. A bana mun tsallake wani siradi mai muhimmanci a tafarkinmu na tabbatar da ci gaban Nijeriya. Zaben da muka yi wa gwamnatin dimokradiyya ta bakwai a jere na nuna cewa kasarmu ta yi riko da tsarin dimokradiyya da aiki da doka.
7. Ranar da na kama mulki na dauki alkawurra kan yadda zan shugabanci wannan babbar kasa ta mu. Daga cikin alkawurran har da yi wa tattalin arzikinmu garanmbawul domin samar da tsaro ga rayuka, ‘yanci, da walwalar al’umma.
8. Na ce daukar tsauraran matakai ya zama wajibi domin dora kasarmu kan tafarkin walwala da bunkasar tattalin arziki. A ranar na sanar da kawo karshen tallafin man fetur.
9. Ina sane da wahalhalun da suka biyo baya. Idanuna suna gani kuma zuciyata ta na kunci. Ina son in bayyana muku dalilin da ya sa wajibi mu ci gaba da daurewa a cikin wannan mawuyacin hali. Wadanda ke son a ci gaba da tallafin man fetur da mummunan tsarin sauyin kudaden waje, mutane ne da ke son gina tafka-tafkan gidaje a cikin fadama. Ni ba haka nake ba. Ni ba zan gina mana gida a bisa tubalin toka ba. Idan muna son gidanmu ya yi kwari to dole ne mu gina shi kan tsandauri.
10. Gyara abu ne mai ciwo, amma shi ne abin da ci gabanmu da daukakarmu ke bukata. A yanzu muna dauke da wahalhalun da za su kai mu zuwa ga makomar da za a raba arzikin kasarmu mai yalwa bisa adalci ga kowa da kowa maimakon wasu tsirarun mahandama su tattare a wurinsu. Zamu samar da Nijeriyar da za a mayar da yunwa, fatara, da wahala su zama tsohon labari.
11. Ba na farin cikin ganin al’ummar kasar nan na fama da wahalar da ya kamata a ce an sauke ta a shekarun da suka wuce. Zan so a ce babu wadannan wahalhalun a yanzu. Amma dole ne mu daure idan muna son samun makoma ta gari.
12. Gwamnatina na yin bakin kokarinta wurin sassauta wannan wahala. Yanzu zan bayyana muku matakan da muke dauka domin rage wannan radadin da magidanta da iyalai ke fama da su.
13. Mun fara daukar matakan sauya tsarin tafiyar da gwamnati domin samar da daidaton tattalin arziki, yaki da hauhawar farashi, bunkasa ayyukan masana’antu, samar da tsaron rayuka da dukiya da kuma tallafa wa talakawa da sauran mabukata.
14. Bisa tattaunawarmu da ‘yan kwadago, ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki, muna gabatar da karin albashi na farko inda za mu kara mafi karancin albashin gwamnatin tarayya ba tare da kara hauhawar farashi ba. A tsawon watanni shida masu zuwa, kananan ma’aikatan Gwamnatin Tarayya za su samu karin Naira Dubu Ashirin da Biyar kowanne wata a albashinsu.
15. Domin kawo ci gaba a yankunan karkara, mun kafa asusun tallafi kan samar da kayayyakin more rayuwa domin jihohi su bunkasa bangarorin da ke da muhimmanci a yankunansu. Tuni jihohi suka karbi kudi domin ba da tallafin sassauta radadin hauhawar farashin abinci da sauran bukatun yau da gobe.
16. Bunkasa tattalin arziki ta hanyar rage farashin sufuri na da matukar muhimmanci. Dangane da haka ne muka bude wani sabon babi a fannin sufuri ta hanyar samar da motocin haya masu amfani da iskar Gas a fadin kasar nan. Wadannan motoci za su caji kudi mai sauki da bai kama kafar yadda ake biya yanzu ba.
17. Ba da jimawa ba kayan aikin sauya motoci masu amfani da fetur zuwa gas za su fara isowa kasar nan saboda mun dauki matakan takaita lokacin da aka saba dauka kafin shigo da su. Kuma za mu kafa wurin bada horo a fadin kasa domin koyarwa da bada sababbin damarmaki ga masu harkar sufuri da kuma masu kafa masana’antu. Wannan lokaci ne mai muhimmanci da kasarmu ta rungumi hanya mafi inganci wurin samarwa tattalin arzikinmu makamashi. Samar da wannan sauyin, kafa sabon tarihi ne.
18. Na dauki alkawarin tsaftace barnar da ta yi wa Babban Bankin Kasa dabaibayi. Wannan aikin an riga an fara. An kafa sabon shugabanci a Babban Bankin. Kuma mai bincike na musamman da na nada na gab da gabatar da rahotonsa kan kurakuran da aka samu a baya da kuma hanyoyin da za a magance afkuwar hakan nan gaba. Daga yanzu, dokokinmu na tasarrufi da kudi za su amfani kowa da kowa ne maimakon masu iko da masu kudi kadai.
19. Dokar haraji mai hikima na da muhimmanci ga ci gaban tattalin arziki da adalci. Na kaddamar da kwamitin sauya fasalin tsarin haraji domin inganta tattara haraji a kasar nan da kuma magance dokoki marasa adalci ko masu kawo tarnaki ga ci gaban kasuwanci da bunkasar tattalin arziki.
20. Domin bunkasa samar da aikin yi da kudin shiga ga mazauna birane, mun samar da asusun zuba jari ga kamfanonin da suka nuna alamar makoma ta gari. Haka kuma mun kara zuba jari a kanana da matsakaitan kamfanoni.
21. Daga wannan watan, za a kara gidaje miliyan 15 kan wadanda ake bai wa tallafin kudi kai tsaye domin rage masu radadi.
22. Gwamnatina a ko da yaushe za ta ci gaba da bai wa tsaron al’umma muhimmancin gaske. Mun bunkasa hadin kai da musayar bayanan sirri tsakanin hukumomin tsaro. An dora wa manyan hafsoshin sojin muhimmin aikin farfado da karsashin rundunonimu.
23. A nan, nake jinjina da yabo ga dakarun tsaronmu, da suke ba mu kariya tare da tabbatar da tsaron kasarmu. Da yawansu sun riga mu gidan gaskiya. Muna tuna su a yau tare da iyalansu. Za mu bai wa dakarunmu kayan aikin da za su sauke nauyin da ke kansu a madadin al’ummarmu.
24. Zamu ci gaba da nada mutane bisa muhimman mukamai daidai da tanadin tsarin mulki na yin adalci ga kowa. Za a cigaba da kulawa da mata, matasa da masu bukatu na musamman a wadannan nade-naden.
25. Zan yi amfani da wannan dama domin taya Majalisun Dokoki na Kasa murna kan rawar da suka taka wurin kafuwar wannan gwamnati ba tare da bata lokaci ba ta hanyar gudanar da ayyukan da tsarin mulki ya dora musu na tantance wadanda za a nada da kuma sa ido kan yadda suke gudanar da ayyukansu.
26. Haka kuma ina taya bangaren Shari’a murna a matsayinsu na ginshikin dimokradiyya da adalci.
27. Ina kuma taya murna ga kungiyoyinmu na ci gaban al’umma da kungiyoyin kwadago bisa sadaukarwarsu ga dimokradiyyar Nijeriya. Ba ko da yaushe ra’ayinmu kan zama daya ba amma ina mutunta shawarwarinku. Ku ‘yan uwana ne kuma ina girmama ku.
28. ‘Yan uwana ‘yan Nijeriya, tsoro ko kiyayya ba za su kawo mana ci gaba ba. Za mu iya samun ingatacciyar Nijeriya ne kadai ta hanyar kwarin gwiwa, tausayi da kuma sadaukar da kai a matsayin dunkulalliyar kasa guda.
29. Na yi alkawari zan ci gaba da mayar da hankali tare da bauta muku cikin amana. Ina kuma gayyatar kowa ya bada gudunmawa wurin ci gaban kasarmu abar kaunarmu. Za mu iya. Ba makawa za mu yi. Kuma tabbas za mu yi nasara!!!
30. Baki dayanku ina taya ku murnar cika shekaru 63 da samun ‘yancin kai.
31. Nagode da sauraro.
32. ALLAH Ya albarkaci Tarayyar Nijeriya.