Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatin tarayya karkashin jagorancinsa tana aiwatar da shirye-shirye da manufofin da za su bai wa ‘yan Nijeriya damar yaki da kalubalen talauci da aikata laifuka da ta’addanci.
Shugaban wanda mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya wakilce shi a wajen bikin kaddamar da faretin horar da dalibai 70 na makarantar horas da sojoji ta Nijeriya (NDA) a jihar Kaduna a ranar Asabar, shugaban ya ce shirye-shiryen wani sabon salo ne da za a fito da shi don samar da tsaro.
- AU Ta Yi Kira Da Kara Zurfafa Dangantakar Dake Tsakanin Kasashen Afirka Da Sin
- Tauraruwar Ronaldo Na Dada Haskawa, Al Nassr Na Ci Gaba Da Jan Zarenta A Saudiyya
A cewarsa, shirin zai kasance ne ta hanyar jajircewa wajen tunkarar kalubalen tsaro da ke barazana ga Nijeriya da yankin yammacin Afirka.
Shugaba Tinubu ya kuma umarci duka shugabannin tsaro na kasar nan da su hada kai a kokarinsu na kare martabar yankunan kasa.
Ya kuma bayyana cewa kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) a karkashin jagorancinsa tana aiki tukuru don inganta harkokin magance rikice-rikice a yankin domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.