• English
  • Business News
Sunday, November 2, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jerin Kasashen Da Ke Fama Da Tsananin Zafin Da Ba A Taba Yi Ba

by Rabi'u Ali Indabawa
2 years ago
Zafi

Kasashe da dama na duniya na ci gaba da fama da tsananin zafi mai hadarin gaske, inda hukumomi ke ba jama’a shawarwari kan irin matakan da za su dauka na kare kai da sauran masu rauni daga illar yanayin.

A wasu kasashen ma ta kai ga ana kwashe mutane daga yankunansu saboda illar gobarar daji, wadda yanayin zafin ke haddasawa.

  • Sin Da Amurka Sun Gudanar Da Taron Tattaunawa Kan Sauyin Yanayi a Birnin Beijing

Tuni kasashe da dama musamman wadanda suke bangaren Arewacin duniya suke fama da wannan matsala ta tsananin zafi da kusan ba a taba ganin irinta ba a baya.

Kasashen su ne na nahiyar Amurka ta Arewa da Turai da yawancin kasashen Asiya da wasu kasashen Arewa maso Kudancin Latin Amurka da kuma Arewacin Afirka.

Kasashen da ke yankin tekun Bahar-Rum na daga cikin wadanda suka fi dandana kudarsu a wannan sauyi na zafi da ake gani.

LABARAI MASU NASABA

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto

Tsawon kwanaki kasashen Italiya da Sifaniya da Girka suke fama da tsananin zafin.
Ma’aikatar lafiya ta Italiya ta yi gargadi da ankarar da jama’a game da illoli da matakan da ya kamata su dauka, domin kariya, a biranen kasar 16, wadanda suka hada da babban birni, Rum da Bologna da Florence.

Kuma hukumomin kasar suna ganin matsalar za ta ci gaba har wannan satin da za a shiga, inda yanayin zafin zai iya kai wa maki 48 a ma’aunin Selshiyas a birnin Sardinia, kamar yadda aka ruwaito a kafafen yada labaran kasar ta Italiya.

Haka kuma ake ganin lamarin zai kasance a sauran sassan Kudancin Turai.
Masanin kimiyyar suffa, kuma tsohon ministan makamashi na Italiya Roberto Cingolani ya gaya wa BBC cewa halin da ke ciki ya sa mutane sun fara fahimtar alakar tsananin sauyin yanayin da ke faruwa da kuma dumamar yanayi a duniya;
Ya ce, tsawon shekaru ana raina matsalar sauyin yanayi da dumamar yanayi, yanzu mun makara.

Ina ganin yawancin gwamnatoci a yanzu suna aiki sosai su rage tasirin sauyin yanayi.
To amma tun da wannan kamar wani yanayi ne ake na gaggawa, sai ya kasance muna ta fama da shi kawai.

Masanin ya kara da cewa, ba ruwan yanayi na duniya da siyasa da wata yarjejeniya da kuma kutungwilar mutane. Ita duniya tana gudana ne yadda take a tsare.

‘’Kuma ina ganin yanzu mun yarda ba wani kokwanto cewa abubuwa na sauyawa, wanda dole kowa ya tashi tsaye ya yi wani abu’’ in ji shi.

Ya kara da cewa ; ‘’A don haka ina ganin watakila duniya za ta koya mana darasi dukkaninmu cewa sai mun kara himma.’’
Haka ake ganin tsananin zafin zai ci gaba ya kai matakin da ba a taba kaiwa ba a sauran sassan Turan ba tare da ganin alamar sauki ba a cikin makon mai shigowa.

A Sifaniya zafin ya haddasa gobarar daji a tsibirin La Palma, da ke kusa da gabar tekun Afirka, inda aka kwashe akalla mutum dubu biyu 2000, yayin da wutar ke ci ganga-ganga.
Ita ma Moroko a bangaren Afirka na wannan yanki na tekun Bahar-Rum ta shiga rukunin da hukumomi ke yi wa jama’a gargadi a kan tsananin zafin.

Haka ita ma Amurka, wadda kashi daya bisa uku na al’ummarta ke cikin tsananin zafin, can a yankinta na Kudu maso Yamma ana fama da zafin sosai, inda a birnin Phoenid, zafin ya wuce maki 43 a ma’aunin Selshiyas, sama da mako biyu.

Hukumomi na gargadin mutane da cewa duk wanda ba shi da wani tanadi kyakkyawa na na’urar sanyaya muhallinsa ko wadata kai da isasshen ruwa to fa yana cikin hadari.

Jamus, ma abin mamaki ba ta tsira daga matsalar ba ta tsananin zafi, inda ‘yan siyasa suka bi sahu na gargadin cewa bala’in sauyin yanayi tuni ya fara hallaka jama’a.

Wasu sassan kasar China da Japan su ma ba su tsira ba daga yanayin na tsananin zafin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga
Kasashen Ketare

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

October 16, 2025
Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto
Kasashen Ketare

Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto

October 7, 2025
Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?
Kasashen Ketare

Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

October 4, 2025
Next Post
Kungiyar Ma’aikatan AKTH Na Da Burin Kafa Bankin Kanta – Abba Yakasai

Kungiyar Ma’aikatan AKTH Na Da Burin Kafa Bankin Kanta - Abba Yakasai

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima

November 1, 2025
Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

November 1, 2025
Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

November 1, 2025
Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya

Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya

November 1, 2025
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

November 1, 2025
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

November 1, 2025
Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

November 1, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar

November 1, 2025
Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

November 1, 2025
Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

November 1, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.