Gwamnatin Jihar Jigawa na ɗaukar matakai domin mayar da jihar cibiyar binciken lafiya, yayin da Gwamna Malam Umar Namadi ya ƙaddamar da ginin manyan cibiyoyin lafiya guda uku a Dutse, babban birnin jihar.
Cibiyoyin da aka fara gina su sun haɗa da Cibiyar Gwaje-gwaje ta zamani (Diagnostic Centre), Cibiyar Kula da Ciwon Zuciya (Cardiac Centre), da kuma Ginin Samar da Iskar Oxygen (Cryo-Oxygen Plant), waɗanda ake sa ran za su inganta harkar lafiya da kuma bunƙasa tattalin arziƙin jihar ta hanyar binciken lafiya.
- Ina Da Ƙwarewar Da Zan Iya Zama Shugaban Ƙasar Nijeriya – Makinde
- Gwamnati Ta Ayyana 18 Da 21 Ga Afrilu A Matsayin Hutun Esta
“Wannan ƙaddamarwar wani babban mataki ne a tafiyarmu na gina Jigawa,” in ji Gwamna Namadi.
“Mun riga mun fara inganta lafiya ta hanyar inshorar lafiya ga marasa ƙarfi da suka haura 143,000 da kuma gina sabbin cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko da na biyu.”
Ya bayyana cewa ko da yake gwamnati ce za ta ɗauki nauyin gina cibiyoyin, daga baya za a miƙa su ga kamfanonin zuba jari na lafiya ta hanyar tsarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu domin tabbatar da ɗorewarsu.
“Waɗannan cibiyoyi ba iya Jigawa za su yi wa amfani ba, har ma da maƙwabta.
“Tare da sabbin na’urorin gwaje-gwaje irin su MRI da mammography, ba sai an je wasu jihohi domin samun irin waɗannan ayyuka ba,” in ji shi.
Gwamnan ya jaddada ƙudirinsa na ci gaba da inganta harkar kiwon lafiya a jihar, ta hanyar samar da sabbin ayyuka daidai da zamani.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp