A ranar 1 ga watan Mayu agogon Paris, hukumar dab’i da harsunan waje ta kasar Sin, tare da hukumomin yayata al’adu na koli da na yankuna, sun halarci bikin baje kolin kasa da kasa na birnin Paris na kasar Faransa na shekarar 2024, kuma sun yi nasarar gudanar da “Gamuwa da kasar Sin” wato jigon bajen kolin al’adun kasar Sin.
Wannan baje kolin ya yi amfani da “Daga al’adun gargajiya zuwa kyakkyawar rayuwa” a matsayin takensa na shekara-shekara, wanda ke nuna dogon tarihin al’ummar kasar Sin, da kyawawan al’adun kasar Sin na musamman, da kuma nasarorin da kasar Sin ta samu a zamanin yau. (Mai fassara: Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp