A Arewacin Nijeriya, akwai Jihar Kaduna; wadda jiha ce mai cike da albarkatu, duk kuwa da cewa; tana fama da matsaloli iri daban-daban da suka hada da yaudara, rashin sanin tsarin gudanar da mulki, rashin gogewa a bangaren sha’anin siyasa da sauran makamantansu. Abubuwan da suka faru na baya-bayan nan, ko shakka babu; sun fallasa karuwar basussukan da suka yi wa jihar katutu, wanda ya tabbatar da ita a matsayin ta biyu wajen tilin bashi mara ma’ana a Nijeriya.
Wani abu da ya fi daukar hankali shi ne, irin rawar da mazaunin gidan fadar mulki na Sir Kashim Ibrahim ya taka, wanda tun kafin hawansa ya jagoranci amincewa da wani gagarumin lamuni daga Bankin Duniya a lokacin da yake majalisar dokoki. A halin yanzu da ya fuskanci illar rashin kudin da zai gudanar da ayyukansa na raya kasa kuma, sai ya koka da rashin wannan kudi; don gudanar da muhimman ayyukan da ya sanya gaba duk kuwa da cewa, jihar na karbar makudan kudade daga gwamnatin tarayya a kowane wata; domin amfanin daukacin al’ummar wannan jiha ta Kaduna.
- Manyan Dabarun Kiwon Zuma A Nijeriya
- Kiwo: Matakai Uku Na Sayar Da Nama Kai-tsaye Ga Abokan Cinikayya
Har ila yau, wani al’amari mai daure kai shi ne, rikita-rikitar siyasa da rudani tare da rashin bin ka’ida tattare da wadannan basussuka, wanda shi ne musababin wannan tabarbarewar rashin kudi da ta kai ga sai da sidin goshi ake iya biyan albashi a jihar a halin yanzu.
Basussukan Da Aka Gada
Gwamnan ya bayyana cewa, ya gaji manyan basussuka daga wurin gwamnatin da ta shude; karkashin jagorancin Malam Nasir elrufai, wanda ya kasance a matsayin mai gidansa, na zunzurutun kudi har dala miliyan 587, wanda ya yi daidai da Naira biliyan 705; idan kowace dala ta tashi a kan Naira 1,200, kamar yadda yake a ranar 3 ga Maris na 2024, sannan da kuma Naira biliyan 85 da kuma Naira biliyan 115 na basussukan ‘yan kwangila.
Tambayoyin da suka dace a wannan gaba su ne:
- Shin wannan bashin ya kunshi kudin albashi ne da ba a biya ba ga ma’aikatan wucin gadi, ko kwangila, ko na ‘yan bautar kasa (NYSC), da dai sauran ma’aikata?
- Shin wannan bashi ya kunshi kudaden albashin da ba a biya ba ga malamai ko ma’aikatan lafiya ko kuma sauran ma’aikatan gwamnati?
iii. Shin wannan bashi ya kunshi hakkin ‘yan fansho ne da sauran iyalan ma’aikatan da suka rasu?
Alkawari Da Yarjejeniyar Da Gwamna Ya Shiga Da Jama’ar Jihar Kaduna
Wannan yarjejeniya ta 2023, ‘The Sustain Manifesto- 2023’’, ya kunshi ajanda ta 7 tare da mayar da hankali kan ci gaban jihar kamar haka: Samar da tsaro, samar da kayan more rayuwa, samar da manyan cibiyoyi da hukumomi, karfafa ciniki da zuba jari, noma, samar da kwararrun ma’aikata tare da inganta rayuwa al’umma
Wani Hanzari Ba Gudu Ba:
- Shin nawa za a kashe wajen aiwatar da wannan ajanda guda 7, sannan kuma a cikin shekaru nawa?
- Shin za a aiwatar da ajanda bakwan kuwa, tun da makuden kudaden da ake karba daga gwamnatin tarayya sun samu nakasu?
- Yaya batun jin dadin al’ummar Jihar Kaduna?
Rashin amsa wadannan tambayoyi guda uku na nuni da cewa, dimokuradiyyar Nijeriya ko shakka babu gurguwa ce maras armashi.
Filin Kalankuwa Da ‘Yan Kama
A karkashin tsarin bayar da bashi ga kasashe masu raunin tattalin arziki (Debt Sustainability Framework for Low-Income Countries), wanda Bankin Duniya da bankin bayar da lamuni (IMF) ke amfani da shi, karbar bashi ya dogara ne da ikon da kasa da jiha ta ke da shi wajen iya sarrafa bashinta ba tare da bukatar lamuni ba ko rage bashi ko jin kasala wajen biyan bashin ba.
Masana na amfani da abin da ake kira (Debt Sustainability Ratio), wato kwatanta matakan ikon biya tare da yin la’akari da samun kudin shiga da kuma habbakar tattalin arziki da sauran alamu a bangare guda da kuma daya bangaren wato (DSA), wannan wani tsari ne na jarrabawa; wanda ke nuni da iya karbar bashi ko rashin iya karba.
Saboda haka, da zarar matakan sun nuna alama mai kyau, gwamnati a kowane mataki tana iya jin cewa; tana da ikon karbar basussuka, amma kash hakan ba daidai ba ne domin ba a nan gizon ke saka ba.
Amfanin wadannan alamomi shi ne, taimaka wa masu bincike wajen tantance hadarin bashin da kuma jagorantar yanke shawara, domin kula da bashin a matakai masu dorewa; amma ba don tara bashi saboda kawai gwamnatin mai dorewa ba ce.
Tatsuniya Ko Makircin Siyasa
A cikin wani yanayi mai daure kai, gwamna mai ci a halin yanzu ya samu kansa a karagar mulkin jihar ba tare da wani kwakkwaran tsari na ciyar da jihar gaba ba.
Yayin da lalitar gwamnati ke matukar fuskantar kalubalen rashin kudi, shi kuma wanda ya yi ruwa ya yi tsaki wajen jajibo wa jihar bashin na fuskantar sakamakon wannan aika-aikar da ya yi, su kuma al’ummar jihar suna cikin tsaka mai wuya; domin kuwa ba su san makomarsu ba, musamman a wajen samun romon dimokaradiyya da sauran ayyukan ayyukan ci gaba.
Wani abin kyama kuma shi ne, yadda makircin siyasa irin na Nijeriya ke jawo wa al’umma rashin cigaba, sannan kuma ya fito fili cewa; son kai na masu madafun iko shi ne ya haifar da wannan tabarbarewar tattalin arzikin jihar, kazalika yana fito da matsalar da ke tsakanin mai gida da yaronsa.
Tabarbarewar Tattalin Arziki Da Jin Dadin Jama’a:
Hukumomin da aka damka wa alhakin kula da jin dadin jama’a tare da samar da tagomashi, tuni sun karkatar da su zuwa hukomin da suka yi kama da aikin kwace. Misali:
I- Hukumar da ke kula da zirga-zirgar ababen hawa da tabbatar da bin doka da oda a jihar, wadda tun farko aka yi wa matsayin wata hukuma mai sa ido da lura, ta koma sana’ar samar da kudaden shiga ga gwamnati, farautar masu ababen hawa marasa galihu tare da tuhume-tuhumen da su kansu sun karya doka, sannan ga cin tarar da ake dora wa ‘yan jihar na karin nauyi a kan wanda suke fama da shi.
II- Haka zalika, ofishin yin rajistar filaye sakamakon gazawa da rashin iya aiki, ya haifar da hasashen wani mulki mai kama da tsarin zamba cikin aminci ga masu zuba hannun jari da harka gine-gine.
Bauta Wa Ma’aikatan Gwamnati
Kamar yadda shafin yanar gizo na Hukumar Kididdiga ta Jihar Kaduna (KSBS) ya nuna cewa, adadin mutanen jihar ya kai kimanin miliyan 10.4 a shekarar 2023. Haka kuma, a wata hira da mallam ya yi wajajen Mayun 2016, ma’aikatan jihar dududu ba su kai 100,000 ba.
Sannan, an yi hasashen
cewa, Jihar Kaduna na samun kimanin Naira biliyan 10, a kowane wata daga asusun gwamnatin tarayya, domin yi wa jama’ar jihar aiki tare da samar da ababen more rayuwa, amma kusan Naira biliyan bakwai na tafiya ne wajen biyan basuka da kuma kudin ruwa, sannan abin da yake saura ba ya wuce Naira biliyan uku kacal.
Babu shakka, wannan ya zama babban kalubale ga jihar; domin kuwa tana bukatar Naira billiyan 5.2 a kowane wata, don biyan albashi ga ma’aikatanta su 100,000. Sannan, abin la’akari kuma shi ne, jama’ar jihar ba sa samun nasu kason; wanda gwamnatin tarraya ta bayar, domin yi musu aikace-aikacen yau da kullum. Saboda Allah wannan wauta har ina!
Baya ga wadannan abubuwa da aka zayyano a sama, wani babban abin takaicin kuma shi ne; yadda wadanda aka damka wa alhakin yi wa al’ummar jihar su kimanin miliyan 10 hidima, ga dukkanin alamu sun juya wa aikin nasu baya, domin kuwa sun fifita jin dadin rayuwarsu ta hanyar biyan kansu kudaden alawus-alawus (ko da yake gwamna ya ce an tsayar) wannan hali ya sake ta’azzara matsalar rashin kudi da jihar ke fama da shi.
Kira a nan shi ne, kamar kidayar makarantu na shekara-shekara, zai dace Hukumar KSBS ta gudanar da kidayar ma’aikatan gwamnati na shekara-shekara.
Watsi   Da Manyan Gobe
A cewar ‘Statisense’, kasafin kudin Jihar Kaduna na shekarar 2024 a bangaren ilimi shi ne, Naira biliyan 115.42b, inda ya sanya ta a matsayi na biyar a jerin jihohin da ke da kasafin kudin ilimi mai gwabi.
- Binciken da ofishin kididdiga na Jihar Kaduna (KSBS) ya gudanar a shekarar 2020 ya nuna cewa, jimillar yara kimanin 768,739 a jihar ba sa zuwa makaranta a matakin farko na ilimi (wato Basic 1 to 9). Wannan kuwa ya kunshi yara 535,353 a matakin firamare da kuma yara 233,386 a matakin kananan makarantun sakandire.
- Kudaden makarantun gaba da sakandire na Jihar Kaduna, sun yi tashin gwauron zabi; ta yadda dalibai da iyayen daliban ba sa iya biyan kudaden makarantar. Kada mu manta da cewa, sama da kashi 98 cikin 100 na wadanda ke cikin gwamnati ko rike da madafun iko, sun sami ilimin karatunsu na gaba da sakandire ne kyauta ba tare da wata damuwa ba. Wannan zalunci har ina!
- Halin da ‘yan jihar ke ciki ya kara ta’azzara ne, sakamakon rashin samun damar karo ilimi, domin kuwa an hana tare da sake tsaurara matakan da za a bi, domin samun tallafin wannan karatu (scholarship), yayin da kuma ka’idojin samun rancen bashin don karo ilmi daga hukumar ba da tallafin karatu da lamuni ta jihar shi ma ya munana kwarai da gaske.
Babban abin ban tsoro shi ne, makomar wadannan dimbin yara da ba sa zuwa makaranta da kuma rashin samun tallafin kudi, domin karo ilimi. Haka zalika, ya rayuwarsu da kuma harkar tsaronsu za ta kasance nan gaba? Al’ummar da babu ilimi, babu shakka tana cikin mummunan hadari.
Masu Ci Da Gumin Addini
Dambarwar siyasa na musulim-musulim tikiti, wanda ya haifar da gwamnatocin da suka shude; ya yi wa mulki karan-tsaye, sannan kuma babu wani alfanu a tattare da wannan dabara. A maimakon haka, ya ci gaba da samar da mulkin da bai dace ba tare da raunata al’umma.
Bugu da kari, dabarun ba su da wani tasiri ko taimakawa wajen magance matsalolin da ke addabar jihar. Ci gaban a nan kawai shi ne, shugabannin addinai na ci gaba da samun tagomashi yayin da jihar kuma ke kara durkushewa.
Hattara Dai
Kimanin kashi 80 cikin 100 na jami’an gwamnatin da ta shude, sun samu kansu a cikin wannan sabuwar gwamnati, hakan na nuni da ci gaba da tsare-tsaren da suka taimaka wajen durkusar da jihar kenan.
Har ila yau, wannan yanayi ya haifar da tambayoyi game da yiwuwar wanzuwar marasa kishin jihar a cikin makarraban wannan gwamnati.
Ina Muka Sa Gaba?
A matsayinmu na masu kula da makomarmu da kuma kishin jiharmu, ya zama wajibi mu yi tsokaci tare da yin fatan da zai haifar mana da canji mai ma’ana, don haka:
- Mai girma gwamna, lokaci ya yi da za a sake yin nazarin wasu dokoki da tsare-tsaren ayyuka, sakamakon tarnakin da suka kawo wajen ci gaba tare da walwalar jama’a.
- A kan maganar bashi kuwa akwai mafita, amma idan aka cire siyasar son zuciya.
iii. Ga wadanda ke wajen Kaduna, wannan kundi ne da za su iya amfani da shi domin dora jiharsu a kan sikeli.
Alhaji Adamu Rabiu ya rubuto daga Kaduna