Mataimakin gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya bayyana cewa gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf za ta hada kai da kwalejin bunkasa fasahar noma na zamani ta gwamnatin tarayya da ke Kono domin inganta harkokin noma.
Mataimakin gwamnan ya bayana hakan ne a lokacin da shugaban kwalejin bunkasa fasahar noma (FCAPT), Dakta Muhammad Yushau Gwaram ya jagoranci kungiyoyin bunkasa tattalin arzikin al’umma suka ziyarci mataimakin gwamnan Kano a fadar gwamnatin jihar ranar Alhamis da ta gabata.
Kwamared Abdussalam Gwarzo ya ce gwamnati Kano karkashin ma’aikatar bunkasa aikin gona ta Jihar Kano, irinsu KANARDA da kamfanin KASCO za su yi aiki kafada da kafada domin samar da ci gaba ta fuskar noma da kuma tsare-tsare na dawo da hukumar siye da siyarwa na amfanin gona wajen samar da kyakyawan yanayi da manoman Jihar Kano za su amfana.
Shi ma shugaban kwalejin FCAPT, Dakta Gwaram ya ce bisa la’akari da cewa kashi 70 na mutanan Jihar Kano sun dogara ne da aikin gona, don haka ne kwalejin ke neman hadin kan gwamnati wajen warware matsalolin da suka addabi manoma, kamar karancin taki da kuma tsadar kayayyaki da sauran matsaloli da manoma ke fuskanta na a ganin an warwaresu.
Ya ce a bangaran kwalejin, yanzu haka sun samar da na’urar sarrafa timatur wanda za a ajiyeshi har shekara guda, sannan suna horar da matasa dabarun noma na zamani domin samun sana’a ta dogaro da kai a wannan lokaci.
A karshe ya yaba wa mataimakin gwamnan kan karbar da ya yi wa wannan ayari na kungiyoyi wanda suka yi taro, wanda shi ne karo na uku a Kano kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta ranar domin tunawa da irin wadanan kungiyoyi na bunkasa tattalin arzikin al’umma.