Gwamnatin Jihar Katsina ta kafa kwamiti don rarraba shinkafar da gwamnatin tarayya ta bayar. Wannan sanarwa ta fito ne daga Kwamishinan yaɗa labarai da Al’adu, Dr. Bala Salisu-Zango, a ranar Litinin a Katsina. Mukaddashin Gwamna Malam Faruk Lawal-Jobe ya naɗa Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Abdullahi Garba-Faskari, a matsayin shugaban kwamitin.
Sauran membobin kwamitin sun haɗa da Mashawarci na Musamman kan Ayyukan Jama’a, Kwamishinonin Ayyuka na Musamman, da wakilin Majalisar Dokokin Jiha, da kuma wasu jami’an ƙananan hukumomi da wakilan hukumomin tsaro, da kungiyoyin addini, da ƙungiyoyin matasa, da kuam ƙungiyoyin farar hula.
- Gwamna Radda Ya Amince Da Bai Wa Ma’aikata N15,000 A Matsayin Goron Sallah
- Katsina United Ta Kammala Ɗaukar Ƴan Wasa Biyu Daga Kano Pillars
Kwamitin zai tabbatar da adadin buhunan shinkafar da aka karɓa daga Gwamnatin Tarayya da kuma tsara yadda za a rarraba shinkafar a fadin ƙananan hukumomi 34 na jihar. Ayyukan su sun haɗa da tabbatar da tsarin rarraba shinkafar cikin gaskiya da adalci, musamman ga marasa galihu kamar gwauraye, zawarawa, da tsofaffi maza da mata.
Dr. Salisu-Zango ya jaddada muhimmancin waɗannan matakai don tabbatar da adalci wajen rarraba kayan ga waɗanda suke da buƙata.
Dr. Salisu-Zango ya kuma bayyana cewa ana sa ran kwamitin zai miƙa rahotonsa cikin makonni uku.
Mukaddashin gwamnan ya tabbatar da cewa jihar ta karɓi manyan motocin shinkafa guda 20 daga gwamnatin tarayya, kuma gwamnatin jiha ta samar da tallafin jigilar kayayyakin don sauƙaƙe rarrabawa zuwa wurare daban-daban a cikin ƙananan hukumomi.