A ci gaba da jigilar dawo da Alhazai gida bayan kammala aikin hajjin bana, a halin yanzu jihohi 11 sun kammala aikin dawo da Alhazansu gida Nijeriya. Jihohin da suka samu wannan nasarar sun hada da Bauchi, Kaduna, Osun, Legas, Borno, Ogun, Binuwai, Kogi, Nasarawa, Edo, Yobe, Filato da kuma Alhazan Jihar Oyo sai kuma bangaren jami’an tsaron Nijeriya.
An samu wannan nasarar ce a daidai lokacin da aka yi kwanaki 17 ana aikin jigilar Alhazan daga kasa mai tsarki zuwa Nijeriya. Jimillar Alhazan da aka dawo da su ya kama 32, 836 wanda ya kama kashi 64 na daukacin Alhazan Nijeriya kenan gaba daya.
- Alhazan Neja Sun Yi Watsi Da Kalaman Gwamna Bago A Kan NAHCON
- Yajin Aiki: NAHCON Ta Gargadi NLC Kan Janyo Cikas Ga Jigilar Maniyyata
Jihohin da ake sa ran za su kammala nasu jigilar a ‘yan kwanakin nan sun hada da Kano, Ondo da Babbar Birnin Tarayya Abuja.
Jihohin Adamawa, Gombe, Jigawa, Katsina da Taraba na shirye shiryen fara dawo da nasu Alhazan zuwa gida, su ne kuma suka kasance na karshe na jiren jigilar Alhazai zuwa kasa mai tsarki.
Mataimakiyar Darakta a hukumar NAHCON Hajiya Fatima Sanda Usara, ta tabbatar da wadanna bayanan a takaradr sanarwar da ta raba wa manema labarai a birnin Makkah.