Gwamnatin tarayya ta dauki tsattsauran mataki game da jihohin da suka zabi rage kudin wutar lantarki, inda ta bayyana cewa; alhakin tallafin da ya dace a biya, ya zama dole ya koma kan jihohin.
Ma’aikatar wutar lantarki, wacce ta bayyana hakan ta bayyana cewa; ba ta da niyyar yi wa hukumomi masu cin gashin kansu katsalandan, amma kuma tana sa ran za su yi la’akari da yadda abubuwa ke kasancewa na zahiri kafin su kai ga yanke shawarar rage wannan kudin wuta.
- Majalisa Ta Ba Wa Shugaban NNPCL Awa 24 Ya Bayyana Gabanta Ko Ta Sa A Kamo Shi
- Tinubu Na Yi Wa Arewa Manyan Ayyuka – Martanin Fadar Shugaban Ƙasa Ga Kwankwaso
Kamar yadda kwamishinan wutar lantarki da sabunta makamashi na Jihar Benuwai kuma shugaban kungiyar kwamishinonin wutar lantarki da makamashi a Nijeriya, Barista Omale Omale, ya kare matakin da hukumar kula da wutar lantarki ta Inugu (EERC), ta dauka na rage farashin wutar lantarki ga kwastomomin kamfanin Rukunin A (Band A) a jihar.
Har ila yau, matakin ya haifar da martani da dama a cikin sashen samar da wutar lantarki a masana’antar, Omale ya ce; tsarin jadawalin biyan kudin wutar yanzu a Jihar Inugu, kamar yadda EERC ta kididdige, ya fi kama da abin da hankali zai dauka.
Hukumar kula da wutar lantarki ta Jihar Inugu ta sanar da cewa, babban kamfanin da ke kula da rarraba wutar lantarki, sabon kamfanin raba lasisi na Jihar Inugu, zai rage farashin Rukunin A (Band A), zuwa Nair 160 kam kowane kwh, maimakon Naira 209 da ake saya, inda kuma Rukunin B zuwa E; za su ci gaba da saya kamar yadda suka saba.
Bayan wannan mataki kuma, jihohi bakwai da suke da ruwa da tsaki kan harkokin wutar lantarkinsu, karkashin dokar 2023; na fuskantar matsin lamba a kan su sake duba kudaden da ake biya na wutar lantakin, bayan hukumar EERC ta fitar da wani muhimmin mataki na rage farashin wutar lantarkin na sashen Rukunin A (Band A), da kashi 24 cikin 100; wato daga Naira 209 zuwa Naira 160, tun daga 1 ga watan Agustan 2025.
Da yake zantawa da LEADERSHIP, mai bai wa ministan wutar lantarki shawara na musamman kan dabarun sadarwa da kafafen yada labarai, Bolaji Tunji ya ce; idan jihohi suka zabi rage kudin wutar lantarki, ya zama wajibi su kasance cikin shiri, don samar da kudaden tallafin da ake samu sakamakon wannan ragi, maimakon kara wa gwamnatin tarayya nauyi da tallafin da a yanzu haka; yah aura sama da Naira tiriliyan biyan a fannin samar da wutar lantarkin.
Har ila yau, ya kuma jaddada cewa; yayin da jihohi ke da ‘yancin cin gashin kai, kan kayyade kudin wutar lantarki, cin gashin kan ya zo ne tare da yin la’akari da abubuwan da suka shafi kudi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp