Kwanaki ne Ofishin Kula da Basuka na Kasa (DMO) ta bayar da kididdgar yawan basukan da ake bin jihohi 36 na kasar nan inda ya ce, basukan da ke bin jihohji 36 da babbar birnin tarayya Abuja ya kai Dala Biliyan 4.61 lamarin kuma yana ta karuwa. An dai fitar da kididigar ne a ranar 31 Disamba 2023.
Bayanin ya nuna cewa, jihohi 10 da suke kan gaba a yawan basuka a Nijeriya sun kasance kamar haka:
Jihar Anambara
Jihar Anambara ce ta 10 a jerin jihohi 10 da ke dauke da yawan basuka a Nijeriya inda take da basukan kasashen waje na Dala miliyan 107.24 a daidai karshen shekarar 2023, wannan ya nuna yadda basukan suka karu daga yadda yake na dala miliyan 103.82 a shekarar 2022.
Jihar Kano
Bashin da ake bin Jihar Kano ya kai Dala miliyan 107.92 a shekarar 2023, wanda hakan ke nuna karin kashi 7.2 na abin da ke bin jihar a shekarar 2022 (Na miliyan 100.67).
Jihar Inugu
Allah ya albarkaci Jihar Inugu da ma’adanin Kwal, bayani ya kuma nuna an dan samu raguwa a basukan da ake bin jihar a kasashen ketare, inda ake binta dala miliyan 120.86 a shekarar 2022 ya kuma ragu zuwa dala miliyan 120.45 a shekarar 2023. Wannan dan raguwar da aka samu yana nuna irin yadda gwamnatin jihar ke alkinta albarkatun jihar.
Jihar Ekiti
Basukan da ake bin Jihar Ekiti ya matukar karuwa. Basukanta na kasashen waje ya kai Dala miliyan 121.05 a shekarar 2023. Amma a shekarar 2022 kudin da ke kan jihar da sunan bashi ya kai Dala miliyan 105.59, abin da ke nuna irin karuwar da aka samu.
Jihar Ogun
Jihar Ogun mai makwabtaka da Jihar Legas da ke tashen bunkasar tattalin arziki tana da basukan kasashen waje da ya kai na dala miliyan 168.83 a shekarar 2023, wannan na nuna karin da aka samu a kan Dala Miliyan 136.26 da ake bin jihar a shekarar 2022.
Jihar Bauchi
Bashin kasashen waje da ke bin Jihar Bauchi ya kai Dala miliyan 187.63 a shekarar 2023, an samu karin ne a kan Dala miliyan 165.78 da ake bin jihar a shekara 2022. Wannan tulin bashin na nuna bukatar da ake da shi na jihar ta kara fadada hanyoyin samar da kudaden shigarta.
Jihar Kros Ribas
Duk da albarkatun kasa da ke jawo masu zuba jari, jihar Kros Ribas ta samu karuwar basukan kasashen waje inda ake binta dala Miliyan 211.13 a shekarar 2023 daga dala miliyan 209.53 da ake binta a shekarar 2022.
Jihar Edo
Bashin kasashen waje da ke a kan Jihar Edo ya tashi zuwa dala miliyan 314.45 a shekarar 2023 daga Dala miliyan 261.15 a shekarar 2022.
Jihar Kaduna
Bashin kasashen waje da ake bin Jihar Kaduna ya kai Dala miliyan 587.07 a shekarar 2023, an samu kari a kan Dala miliyan 573.74 da ake binta a shekarar 2022.
Jihar Legas
Jihar legas ne a kan gaba a jihohin da suke dakon basukan kasashen waje inda a shekarar 2023 ake binta dala biliyan 1.24. an dan samu raguwar bashin ne inda a shekarar 2022 ake bin jihar Dala biliyan 1.25. wannan raguwar da aka samu ya faru ne saboda yadda jihar ta koma dogaro da basukan cikin gida wanda a halin yanzu ya kai Naira tiriliyan 1.05.