Attajirin dan kasuwar jihar Kano, Alhaji Aminu Dantata ya rasa daya daga cikin jikokinsa, Batulu Alhassan Baba Ahmad Dantata.
Batulu ta rasu a Kano tana da shekaru 40 bayan ta sha fama da cutar sikila.
- Nijeriya Ta Yi Nasara A Kotun Ingila Kan Rikicinta Da Kamfanin P&ID
- An Bude Taron Wakilan Mata Na Kasar Sin
Marigayiyar, wacce ta kammala karatun aikin lauya, ta rasu ta bar mahaifiyarta, Hajiya Ummul Khair Aminu Dantata, wadda ita ce diyar farko ga Alhaji Aminu Dantata da mahaifinta, Alhaji Baba Alhassan Ahmad Dantata.
Za a yi jana’izarta a masallacin Juma’a na Koki da ke cikin birnin Kano da misalin karfe 10 na safiyar ranar Talata.
LEADERSHIP ta ruwaito cewar, inda ba a manta ba Alhaji Aminu Dantata ya rasa matarsa ta biyu Hajiya Rabi a cikin watan Afrilun shekarar nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp