Bayanan da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar a jiya Laraba, sun nuna cewa, a shekarar 2023, jimillar kayayyakin yau da kullum da aka sayar a kasar Sin, ta kai Yuan triliyan 47 da biliyan 149 da miliyan 500, wato karuwar kaso 7.2 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.
A yayin taron manema labaran da ofishin labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya kira a wannan rana, shugaban hukumar Kang Yi ya ce, yayin da tattalin arzikin kasar ke ci gaba da farfadowa, yanayin aikin yi gaba daya ya inganta, ana sa ran yawan kudin shigar jama’a zai ci gaba da karuwa yadda ya kamata. Lamarin da zai taimakawa jama’ar kasa wajen kara karfinsu na yin sayayya. Hukumomin sassan kasar Sin za su ci gaba da dukufa wajen farfado da kuma habaka harkokin saye da sayarwa, da fitar da jerin matakai domin sa kaimi ga jama’ar kasa wajen yin sayayya, ta yadda za a tabbatar da yanayin kwanciyar hankali a cikin kasuwannin kasar, da ba da gudummawa wajen farfado da harkokin kasuwanci a cikin kasa. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)