Hare-haren da rundunar sojin saman Operation Hadin Kai (OPHK) ta kai a ranar Asabar, 14 ga watan Oktoba, 2023 a Bukar Meram a jihar Borno ya yi sanadin mutuwar ‘yan ta’adda da dama tare da lalata manyan motocinsu da bindigu guda shida da babura 40 wadanda suka shirya amfani da su don kai hari kan sojoji.
Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar sojin saman Nijeriya, Air Cdre Edward Gabkwet, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce an ba da izinin kai harin ne bayan samun bayanan sirri da gano wata sabuwar maboyar ‘yan ta’adda bayan sun yi kaura daga Suwa zuwa Bukar Meram kusa da yankin tafkin Chadi.
- An Kama Masu Laifi 537, An Daure 250 Cikin Wata 3 A Borno
- Yadda Budurwa Ta Rungumi Fasahar Gyaran Wayoyi A Borno
Hukumar leken asirin ta bayyana cewa komawar ‘yan ta’addar daga Suwa zuwa babban yankin Bukar Meram “shiri ne na sake kai hare-hare kan sojojin kasa da mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
Sakamakon haka, an ba da izinin kai hare-hare ta sama a wurin da ke Bukar Meram domin murkushe ‘yan ta’addar.
Kakakin NAF ya ce: “Sakamakon da aka samu bayan harin ya nuna cewa an cimma sakamakon da ake sa ran gani na kashe ‘yan ta’adda da dama yayin da aka lalata babura sama da 40 da manyan motoci da bindigu 6, wanda hakan ya kashe karfinsu na kai hari kan sojojin kasa da kuma ‘yan Nijeriya da ba su ji ba ba su gani ba.”
Sanarwar ta ce an kai hare-hare makamancin wannan kan ‘yan ta’adda a safiyar ranar 11 ga watan Oktoban 2023 da rundunar sojin sama ta Operation Haradin Daji ta kai a kewayen Sangeko a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.