Hukumar lura da jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC) ta tabbatar da cewa daga ranar Laraba, 1 ga Oktoba, 2025, za a dawo da zirga-zirgar jirgin ƙasa na fasinjoji a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna. Wannan na zuwa ne bayan dakatar da tafiye-tafiye a watan Agusta sakamakon hatsarin da ya rutsa da ɗaya daga cikin jiragen.
A cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Callistus Unyimadu, ya fitar, NRC ta ce matakin ya nuna jajircewarta wajen tabbatar da tsaro da kuma inganycin sufuri ga ’yan ƙasa. Hukumar ta bayyana cewa ranar Laraba za ta kasance rana ta Musamman domin yin gyara a kan layin jirgin don gujewa matsaloli a nan gaba.
- NRC Ta Dakatar Da Sufurin Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna Bayan Hatsarin Da Ya Yi
- Hukumar NRC Ta Dakatar Da Zirga-zirgar Jiragen Kasa Na Abuja zuwa Kaduna
Idan za a tuna, hatsarin da ya faru ranar 26 ga Agusta, 2025, ya shafi fasinjoji 583, inda aka tabbatar da cewa an tuntuɓi mutum 530 daga cikinsu ta waya, sannan aka mayarwa 512 da kuɗinsu. Haka kuma, fasinjoji 22 da suka samu rauni sun samu kulawa daga likitocin NRC, tare da damar tafiya kyauta sau ɗaya a kowane mako har zuwa 31 ga Disamba, 2025.
Hukumar ta kuma sanar da cewa dukkan fasinjojin da suka kasance cikin jirgin a lokacin hatsarin za su samu damar yin tafiya kyauta sau ɗaya kafin ƙarshen shekarar. NRC ta gode wa ’yan Nijeriya musamman masu amfani da jiragen ƙasa kan yadda suka nuna haƙuri, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da inganta tsarin sufuri a faɗin ƙasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp