A ranar Juma’a 6 ga watan nan, babban jirgin ruwa mai samar da hidimar jinya na kasar Sin, wanda ake kira da “Peace Ark”, wato “Jirgin Ruwan Tabbatar Da Zaman Lafiya” a Hausance, ya isa kasar Djibouti dake gabashin nahiyar Afirka, inda zai yada zango na kwanaki 7, tare da samar da hidimomin jinya ga jama’ar kasar.
Babban jirgin ruwan na rundunar sojojin kasar Sin, na gudanar da aiki mai taken “Tabbatar da Zaman Jituwa a shekarar 2024”, kuma ziyararsa a kasar ta Dibouti wani bangare ne na aikin. (Bello Wang)