Babban jirgin sama samfurin C919, wanda kasar Sin ta kera, ya kammala jigilar fasinja na farko daga birnin Shanghai zuwa Beijing a yau Lahadi, wanda ya alamta shigarsa kasuwar sufurin jiragen saman fasinja.
Jirgin, wanda ke aiki karkashin kamfanin jiragen sama na China Eastern Airlines ya tashi ne da lakabin MU9191 da misalin karfe 10:32 na safiya, daga filin jirgin sama na kasa da kasa na Hongqiao dake Shanghai, dauke da fasinjoji 128.
An yi wa jirgin maraba ta hanyar watsa ruwa yayin da ya sauka a filin jirgin sama na kasa da kasa na Beijing da misalin karfe 12:31 na rana a yau Lahadi.
Jirgin na C919 shi ne babban jirgin na farko na jigilar fasinja da Sin ta samar da kanta bisa matakin ingancin kera jirgin sama na duniya, haka kuma yana da shaidar hakkin mallakar fasaha nasa na kansa.
An fara aikin samar da samfurin jirgin na C919 ne a shekarar 2007. An gabatar da jirgin wanda kamfanin kera jiragen sama na kasar Sin COMAC ya samar a karon farko ne a watan Nuwamban 2015 a birnin Shanghai. A kuma shekarar 2017, jirgin ya yi nasarar tashinsa na farko.
A cewar daraktan kula da harkokin talla da cinikayya na kamfanin COMAC, jigilar fasinja ta farko da sabon jirgin ya yi ya nuna cewa ya kai matsayin fara aiki, kuma zai ci gaba da ingantuwa idan ya samu tagomashi a kasuwa. (Fa’iza)