Tun a ranar kaddamar da shi, wasu kafofin yada labarai suka yi ta tsokaci kan cewa asalin jirgin na kasar Ethiopia ne.
Jirgin da Nijeriya ta kaddamar a watan Mayu shatar shi aka yi daga kasar Ethiopia, kamar yadda Shugaban kamfanin jiragen saman Nijeriya, Kyaftin Dapo Olumide ya fada a ranar Talata.
- Hadin Gwiwa Tare Da Sin Zai Taimakawa Sabuwar Gwamnatin Najeriya Wajen Cimma Burin Ta
- Majalisa Ta 10: Gwamnoni 25 Sun Mara Wa Akpabio Da Barau Baya
A ranar 26 ga watan Mayu jirgin na Nigeria Air ya baro Addis Ababa ya sauka a filin tashin jirage na Nnamdi Azikwe da ke Abuja kamar yadda Leadership Hausa ta rawaito.
Sai dai yayin da yake ba da ba’asi a gaban kwamitin Majalisar Dattawa, Kyaftin Olumodi, ya ce jim kadan bayan kaddamar da jirgin, an mayar da shi kasar ta Ethiopia.
Tun a ranar kaddamarwar, wasu kafofin yada labarai suka yi ta tsokaci kan cewa asalin jirgin na kasar Ethiopia ne.
Shugaban kwamitin na majalisar Dattawa, Sanata Biodun Olujimi, ya nuna takaicinsa kan yadda tsohon Ministan Sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya yi hanzarin kaddamar da jirgin a rana ta karshe da Buhari zai kammala wa’adin mulkinsa.
A nasa bangaren, shugaban kwamitin kula da sufurin jirage a Majalisar Wakilai, Nnolim Nnaji, ya kwatanta lamarin a matsayin zamba cikin aminci.
Sai dai ma’aikatar sufurin jirgin saman Nijeriya yayin mayar da martani, ta ce an kaddamar da kamfanin ne ba wai an ce ya fara aiki ba ne.
A cewar Olumide, an yi haka ne don a tunatar da ‘yan Nijeriya cewa aikin kaddamar da kamfanin yana nan ba a manta da shi ba.