Jirgin yakin sojojin sama ya hallaka kasurgumin dan bindiga, Abdulkareem Lawal, da aka fi sani da Faca-faca tare da yaransa.
Lamarin ya auku ne a lokacin da jirgin ya yi luguden wuta ta sama a maboyar ‘yan bindigar da ke hukumar Safana da ke a jihar Katsina.
- RTEAN Za Ta Tabbatar Da Nasarar Samar Da Motoci Masu Amfani Da Iskar Gas A Nijeriya —Musa Maitakobi
- Matsalar Tsaro: An Gudanar Da Addi’oi Na Musamman A Yankin Funtuwa
Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar Gambo Isah, ya tabbatar da hakan a cikin sanarwar da ya fitar, inda ya kara da cewa, jirgin ya kuma kashe wasu ‘yan bindigar takwas ciki har da Faca-faca.
Gambo, ya ce, jami’an ‘yan sanda na rundunar a daren ranar da ta gabata sun sun kai hari a wata maboyar ‘yan bindigar da ke a anguwar Dako a kauyen Tandama cikin karamar Danja a jihar ta Katsina inda suka kubutar da wasu mutane shida da aka sace su.
Ya sanar da sunayen wadanda aka kubutar Alhaji Garba Dan Mallam dan shekara 52, Rabiu Idris dan shekara 45 da kuma Abba Samaila dan shekara 38 wadanda dukkan su, mazuna ne a Unguwar Nuhu.
Sauran sune, Yunusa Sani dan shekara 54, Ishaq Yakub dan shekara 40 Danjuma Samaila dan shekara 45 wadanda dukkan su mazuna ne a kauyen Layin Sani da ke a karamar hukumar Kafur.