A kwanakin baya ne, jakadun kasashe 25 da suka hada da Dominica da Myama da Iran suka ziyarci birnin Urumqi da yankin Kashgar da birnin Aksu na jihar Xinjiang ta kasar Sin tsakanin ranakun 31 ga watan Yuli zuwa ranar 4 ga wannan wata, bisa gayyatar da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta yi musu, inda suka yi musaya mai zurfi da mazauna biranen ’yan kabilu daban daban, tare kuma da ganin ci gaban tattalin arziki da zaman takewar al’umma dake Xinjiang ba tare da wani shamaki ba.
Galibin jakadun sun bayyana cewa, akwai zaman jituwa a tsakanin al’ummar Xinjiang, tattalin arzikin jihar yana samun ci gaba cikin sauri, al’adun jihar sun inganta yadda ya kamata. Bugu da kari, al’ummar Xinjiang na jin dadin rayuwarsu, jita-jitar da wasu kafafen watsa labarai na kasashen yamma suke bazawa ba su dace da hakikanin yanayin da Xinjiang ke ciki ba.
’Yan tawagar sun kuma bayyana cewa, jihar Xinjiang da suka gani da idanunsu, ta sha bamban da yadda wasu kafafen yada labarai na yammacin duniya suke bayyana jihar Xinjiang, mai al’umma dake zaman jituwa, da tattalin arziki mai wadata, jama’ar dukkan kabilu suna zaune lami lafiya, kana ana kara yin ayyuka daban-daban.
Ban da wannan kuma, ’yan tawagar sun shaidawa taron manema labaran da aka shirya bayan kammala wannan muhimmiyar ziyara cewa, musulman Xinjiang suna da ’yancin gudanar da addini bisa doka, maganar cewa wai ana kisan kare dangi da zaluncin addini karya ce kawai aka kitsa da nufin bata sunan kasar Sin mai kaunar wanzar da zaman lafiya da samun bunkasuwa a duniya. A cikin ’yan shekarun da suka gabata, gwamnatin jihar Xinjiang ta yi kokari matuka domin yaki da ta’addanci bisa doka, kuma ta samu sakamako a zahiri.
Sanin kowa ne cewa, burin kafofin watsa labaran yammacin duniya shi ne, jirkita gaskiya game da kasashen da suke adawa da ita, ko dai suke ci gabansu ko burinsu na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da samun wadata a duniya baki daya.
Jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta, wani bangare ne na kasar Sin mai kunshe da kabilu daban-daban dake zaune cikin zaman lafiya da jituwa. Amma saboda adawa da jerin abubuwan dake faruwa da wadansu da ba su taba zuwa yankin ba, suke kokarin baza karairayi da yada jita-jita.
Don haka, bai kamata ba mutane ko kasashe su rika fadin abin da ba su da masani a kai, don kawai neman biyan bukatunsu na siyasa. Gani da ido aka ce maganin tambaya, har ma ya kori ji. (Ibrahim Yaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp