Shugaban Amurka Joe Biden, ya sanar da cewa zai sake tsayawa takara a zaben 2024, inda mai yiwuwa ya sake yin takara da tsohon shugaban kasar, Donald Trump.
An yi tsammanin jam’iyyar Democrat za ta sake neman wa’adin mulki na biyu tsawon shekara hudu tare da kaddamar da yakin neman zabensa a wani bidiyo a ranar Talata.
- Za Mu Tabbatar An Kwaso Daliban Da Suka Makale A Sudan -Gwamnatin Tarayya
- Basarake Ya Mutu A Hannun ‘Yan Bindigar Da Suka Sace Shi A Kogi
Ya ce wannan muhimmin lokaci ne da zai sake bayyana aniyrasa ta sake neman mulkin Amurka.
Mataimakiyar shugaban kasar, Kamala Harris, mai shekaru 58, ita ma ta nuna aniyar sake zama abokiyar takararsa.
Biden, mai shekaru 80, shi ne shugaban kasa mafi tsufa a tarihin Amurka, kuma da alama zai fuskanci tambayoyi kan shekarunsa a tsawon lokacin yakin neman zabe.
Zai kasance mai shekara 86 bayan kammala wa’adinsa na biyu a mulkii cikin shekara ta 2029.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp