Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya isa birnin Accra, na Ƙasar Ghana, domin halartar taron Democracy Dialogue na 2024 da Gidauniyarsa ta shirya tare da haɗin gwiwar gwamnatin ƙasar.
Taron na bana, mai taken “Dalilan Da Ke Sa Dimokuraɗiyya Ta Mutu”, zai haɗa shugabanni da masana don tattauna ci gaba, ƙalubale, da makomar dimokuraɗiyya a Yammacin Afirka.
- Hadin Gwiwar Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Makamashi Tsakanin Sin Da Rasha Ba Abun Zargi Ba Ne
- Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
Jonathan ya ce yana fatan wannan tattaunawa za ta ƙarfafa dimokuraɗiyya a yankin tare da kawo zaman lafiya, tsaro da kyakkyawan shugabanci.
Taron Democracy Dialogue ya zama muhimmin dandali a kowace shekara a Yammacin Afirka don tattauna makomar dimokuraɗiyya, inda a baya ya kan jawo ’yan siyasa, ƙungiyoyi, da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa.
A wannan karon ana sa ran waɗanda za su halarci taron za su tattauna muhimman batutuwa da suke damun yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp