Tsohon kocin Real Madrid da Chelsea Jose Mourinho, mai shekaru 62, ya maye gurbin Bruno Lage wanda aka kora daga aikinsa na kocin kungiyar kwallon kafa ta Benfica bayan rashin nasara da suka yi a wasansu da Qarabag a gasar zakarun Turai ranar Talata, Mourinho ya taba aikin horar da Benfica shekaru 25 da suka gabata.
Tsohon kocin na Chelsea ya koma aiki ne kasa da wata guda bayan da Fenerbahce ta sallame shi sakamakon rashin nasarar da ya yi a wasan neman gurbin Gasar Zakarun Turai da suka buga da sabuwar kungiyarsa ta Benfica, Mourinho ya taba aikin horar da Benfica a shekarar 2000 amma ya jagoranci wasanni 10 kacal kafin ya bar kungiyar bayan takaddama da shugaban kungiyar na wancan lokacin.
Benfica ta kori Lage duk da cewa wasa daya kacal a cikin 6 da suka buga aka doke shi a wannan kakar wasannin ta bana, Mourinho zai karbi aikin horar da Benfica wadda ta ke matsayi na 6 a teburin babbar gasar kwallon kafa ta Portugal, yayinda maki 5 ke tsakaninsu da FC Porto wadda ke jan ragamar teburin, wasansa na farko a kulob din ma Lisbon shi ne na ranar Asabar inda zasu ziyarci AVS dake matsayi na 17.
Mourinho ya yi suna ne a lokacin da yake tare da Porto tsakanin shekarun 2002 zuwa 2004 inda ya lashe kofuna shida, ciki har da gasar zakarun Turai a shekarar 2003-04, tun da ya bar kasarsa a shekara ta 2004, Mourinho ya jagoranci Chelsea, Inter Milan, Real Madrid, Manchester United, Tottenham Hotspur, Roma da Fenerbahce, bayan korar Lage a ranar Talata, shugaban Benfica Rui Costa ya ce dole ne sabon kocin ya kasance yana da kwarewa da gogewa a wannan bangaren.