Julen Lopetegui ya amince da karbar ragamar horas da kungiyar kwallon kafa ta West Ham United, bayan raba gari da David Moyes.
Lopetegui bai sanya hannu kan kwantiragi da kungiyar ba, amma ya bayar da tabbacin karbar aikin kungiyar a karshen wannan kakar wasannin.
- Sabon Babin Diflomasiyyar: Kira Ga Hadin Kai Da Zaman Lafiya
- Yanzu-yanzu: Shettima Ya Dakatar Da Tafiyarsa Zuwa Amurka Saboda Matsalar Jirgi
Matakin wanda ita kanta West Ham ta sanar na zuwa ne a wani yanayi da manajan kungiyar, David Moyes ke tsaka mai wuya bayan rashin nasara a wasanni takwas da ta yi a baya-bayan nan.
A ranar Lahadi ne, Chelsea ta yi wa West Ham wankin babban bargo, inda ta zuba mata kwallaye biyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp