Kasar Sin, mai mafi yawan jama’a a duniya na samun ci gaba mai ban mamaki a fannin fasahar inganta muhalli bisa yadda take bullo da sabbin hanyoyin kare muhalli da amfani da albarkatu yadda ya kamata. Ci gaban da take samu a wannan bangare na da ban sha’awa da kuma uwa-uba kyakkyawan tasiri ga makomar duniyarmu.
Kasar ta mayar da hankali kan makamashin da ake sabuntawa wanda ake samarwa daga abubuwa na asali kamar rana, iska, da ruwa. Kasar Sin ta zama kan gaba a duniya wajen amfani da makamashin da ake iya sabuntawa, musamman hasken rana da iska. Ya zuwa shekarar 2023, kasar ta kaddamar da amfani da hasken rana mai yawa a cikin gida kuma ita ce ke da kaso 50 cikin dari na adadin karfin kayayyakin samar da wutar lantarki ta iska a duniya.
Haka nan, bangaren motocin makamashin lantarki (EVs), wani sashe ne da kasar Sin ke samun ci gaba mai ban mamaki. Motoci ne da ke amfani da wutar lantarki maimakon man fetur, inda suke rage gurbata yanayi da dogaro da albarkatun mai. Kasar Sin ta zama cibiyar wasu manyan masana’antun kera motocin ta duniya kuma tana ci gaba da kakkafa tasoshin cajin motoci a sassanta domin karfafa amfani da wadannan motoci mafi dacewa da muhalli. A shekarar 2024, ta kera motoci masu amfani da sabbin makamashi fiye da miliyan 12. Kazalika, a shekarar 2023, kamfanonin kera batirin motocin na kasar sun sami ciniki a kasuwannin duniya da kaso 60 cikin dari, yayin da kuma suka samu karin kaso 30 cikin dari na adadin baturan da suke fitarwa zuwa waje a bisa mizanin shekara. Amfani da wadannan motocin na lantarki yana taimakawa wajen rage hayaki mai cutarwa da inganta lafiyar muhallin da kowa ke rayuwa a ciki.
Har ila yau, kasar Sin tana zuba jari mai kaurin gaske a fannin tsara birane mafi dacewa da lafiyar muhalli wanda ya kunshi zayyana birane da sauran garuruwa ta hanyoyin da za su dore da kuma tabbatar da kare muhalli. Misali, akwai sabbin gine-gine da yawa a kasar Sin da aka sanya masu koren rufi, wadanda aka lullube da tsirrai da ke taimakawa wajen tsotse ruwan sama, da rage zafi, da inganta yanayin iska. Bugu da kari, biranen kasar Sin sun dukufa kyautata zirga-zirgar jama’a, da hawan keke, da tafiya da kafa don rage cunkoson ababen hawa da gurbacewar yanayi.
Wani muhimmin al’amari na juyin-juya-halin kyautata lafiyar muhalli na kasar Sin shi ne dabarun sarrafa shara. Kasar na aiwatar da tsare-tsare don rage yawan sharar da kuma sake amfani da ita. Wannan yana taimakawa kwarai wajen rage yawan sharar da ake jibgewa a wurare da karfafa tattalin arziki mai kewayowa.
Jarin da kasar Sin ke zubawa wajen inganta lafiyar muhalli mai dorewa a duniya ya nuna muhimmiyar rawar da take takawa ta wannan fuskar. A shekarar 2024, kasar ta jagoranci duniya wajen zuba jarin sauya makamashi, inda ta zuba dalar Amurka biliyan 818 a wannan bangare. Wannan jarin ya sanya kasar Sin ta zama cibiyar samar da makamashi mai tsafta a duniya domin ita ke da kusan kashi 50 cikin dari na tasoshin samar da man “hydrogen” mara gurbata muhalli a duk duniya.
Kasar Sin ta nuna wa duniya kyakkyawan misali abin koyi kamar yadda Shugaba Xi na kasar ke ci gaba da yayata muhimmancin kiyaye halittun doron kasa da kuma maye makamashi mai gurbata muhalli da mai tsafta. Shi ya sa ficewa daga yarjejeniyar shawo kan sauyin yanayi da Amurka ta yi kwanan nan, babban abin kunya ne a huldar da ta shafi kasashen duniya.
Alfanun kiyaye lafiyar muhalli bai tsaya kawai ga kiwon lafiyar halittu ba, ya kuma kunshi bude sabbin damammaki na ayyukan yi da bunkasa tattalin arziki. Hakika, yana da ban sha’awa, a ga manyan kasashe suna kara yin hobbasa wajen samar da kyakkyawar makoma mai dorewa ga dukkan bil’adama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp