Manyan hafsoshin tsaron (ECOWAS) za su sake yin wata ganawa ta musamman a kasar Ghana don ci gaba da tattauna yiwuwar amfani da karfin soja, a kan sojojin Nijar, musamman a yanzu da suke barzanar hallakar da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum.
Tun farko dai an shirya wannan taro ne a ranar Asabar din da ta gabata, amma aka dage shi bayan da shugabannin kungiyar suka amince da fara aikewa da sojoji Jamhuriyar Nijar don tabbatar da mayar da dimokuradiyya kasar.
- Jakadan Argentina: “Ya San Mene Ne Abubuwan Da Jama’a Ke Bukata”
- Lalacewar Hanyar Bauchi Zuwa Gombe Ta Zama Tarkon Mutuwa Ga Matafiya – Gwamna Inuwa
Har yanzu dai matsayar da ECOWAS ke dauka na ci gaba da rikitar da mutane, la’akari da yadda ta ke shan alwashin amfani da karfin soji, a wasu lokutan kuma ta ce akwai bukatar a yi amfani da tattaunawar diflomasiyya, kamar yadda ta fada a taronta na ranar Alhamis din da ta gabata.
Har yanzu dai babu wani tabbas a game da matakin da kungiyar za ta dauka, yayin da gwamnatin sojin Nijar din ke ci gaba da nade-nade da kuma kafa cikakkiyar gwamnati.
A yanzu dai Nijar na karkashin takunkuman ECOWAS da kuma wasu kasashen duniya.