Shugaban kasa Bola Tinubu ya tattauna da gwamnonin jihohin da ke kan iyaka da Jamhuriyar Nijar a yammacin ranar Lahadi.
Taron dai an yi shine yayin da wa’adin da kungiyar ECOWAS ta gindaya wa jami’an sojin Nijar ya cika.
ECOWAS ta bukaci sojin Nijar da su maido da ragamar mulki ga gwamnatin shugaba Mohammed Bazoum da suka hambarar cikin mako guda ko kuma su fuskanci tawagar sojin Kungiyar.
Mahalarta taron sun hada da gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu; Gwamnan jihar Jigawa, Umar Danmodi; Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni; Gwamnan jihar Kebbi, Idris Nasir, da gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda.
Har yanzu dai ba a fitar da wata sanarwa ba kan ganawar da shugaban kasar ya yi da gwamnonin jihohin ba, wacce aka gudanar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp