A matsayin ECOWAS na hukuma, an kafa ta ne domin bunkasa tattalin arziki tare da samar da hadin kai da kuma kyautata rayuwar al’ummar da ke tsakanin su. Amma manya-manyan dalililan kafa wannan gungiya sun hada da kamar haka:Â
Na farko, samar da daidaito da kuma taimakekeniya a tsakanin kasashen. Na biyu, tabbatar da hadin kai tare da samar dokoki na bai-daya a tsakanin su. Na uku, kyautatawa tare da dogaro a tsakaninsu. Na hudu, tausayawa da kuma lallaba juna. Kana na biyar, tabbatar da zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali.
Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), wadda aka kafa a 28 ga watan Mayun 1975, na da mambobi na kasashe goma sha biyar, a lokacin da aka kafa ta a Jihar Legas.
A matsayin ECOWAS a kungiya mai rajin samar da zaman lafiya da kwantar da tarzoma, ta tura dakarun Sojoji Kasashen Afirka daban-daban domin samar da zaman lafiya tare da kwantar da tarzoma a da, yanzu kuma za ta dirar wa Kasar Nijar da yaki.
Aikin da aka san ECOWAS da shi na tabbatar da samar da zaman lafiya da kwantar da tarzoma a tsakanin mambobinta, yanzu ya canza salo ya koma farautar su, duk dai da cewa da su da ke kokarin shiga tsakanin (ECOWAS) da kuma Sojojin da suka yi juyin mulkin, ba a doron demokradiyya suke ba. Sojojin sun saba wa demokradiyya, haka nan su ma masu kallon kawunansu a matsayin hukuma ko masu son kare muradan kawunansu.
Har ila yau ECOWAS din ta karkasu, a cikin kasashe goma sha biyar takwas ne ke kalubalantar Sojojin da suka yi juyin mulkin Nijar, amma sauran ko dai ‘yan babu ruwanmu ko kuma wadanda ke koyan bayan Nijar din kasashe kamar su Mali, Burkina Faso, Guinea da kuma Chadi, babu wani abu da suka aiwatar na rashin goyon baya ko rashin amincewa a kan wadannan Sojoji na Nijar, illa neman ba’asi na shiga tsakanin tun da farko.
Dalilin shiga tsakanin ko dagewa da Shugabannin ECOWAS din suka yi kan Nijar, domin nema wa kawunansu kariya ne sakamakon gazawarsu da kuma kashin da ke gindinsu. Wannan ce ta sa hantarsu ta kada suka shiga firgici, suke neman kariya tare da yunkurin shiga yaki na babu gaira babu dalili.
Haka zalika idan har aka sake aka shiga wannan yaki, Nijeriya ma ba za ta taba kubuta ko tsira ba, sakamon kusancin da ke tsakanin da Nijar da kuma boyayyen sirrin da ke tsakan su, kamar misali katse wutar lantarki wanda ita Nijar za ta iya samar da nata dam din wanda ka iya haifar wa da namu matsala. Don haka, alakar da ke tsakanin Nijeriya da Nijar na da karfin gaske, amma a haka ake tunanin a sa kafa a shure kawai don biyan bukatar kai da neman kariya, indai har Kasashe irin su Burkina Faso, Mali, Guinea da Chadi ba a sanya musu takunkumi ba, ya kamata ita ma Nijar a yi mata adalci a ba ta hakkinta na cikakkiyar kasa mai iko tare da ‘yanci kamar yadda sauran suke da shi.
Bai kamata mu manta cewa, Mohammad Bazoum tubabben Shugaban Kasar ta Nijar wanda ECOWAS ke son a maida wa mulki a hannunsa na hannun Sojojin da suka yi juyin mulkin ba, sannan akwai yarjejeniya a tsakanin su, saboda haka, abu mai sauki su yi garkuwa da shi. Abu mafi sauki a nan shi ne, ECOWAS ta janye dukkanin wata barazana ta tattara hankalinta wajen ganin yadda za a samu maslaha cikin ruwan sanyi don kawo karshen wannan al’amari. Idan kuwa ta gaza yin hakan, zai yi matukar wahala kungiyar ta samu hadin kan mambobinta a matsayin tan a hukuma. Babban burin ECOWAS shi ne ganin an samu zaman lafiya tare da kawar da Sojoji a Nijar su kuma tabbatar da babu abin da ya samu Shugaba Bazoum da sauran iyalansa tare da ci gaba da rayuwarsu cikin jin dadi da annashawa ba tare da an hallaka su ko wani abu makamancin haka ba.
Abraham James, Kwararre ne a kan sadarwa da harkokin Difilomasiyya da ke Nijeriya