Gwamnatin Jihar Kano ta buƙaci Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya ba da umarnin cire Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, daga fadar Nasarawa, tana mai gargadin cewa kasancewarsa a wurin na haddasa tashin hankali a jihar.
Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi wannan kiran ne a yayin rabon kayan tallafi da Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Tarauni, Hon. Kabiru Dahiru Sule, ya bayar.
- Jami’ar Bayero Ta Shirya Bikin Yaye Ɗalibai Karo Na 39
- Gwamnatin Kano Za Ta Ɗau Nauyin Ɗalibai 1,002 Domin Karatu A Ƙasashen Waje
Ya buƙaci Shugaban ƙasa ya ɗauki mataki cikin gaggawa, yana mai cewa “muna kira ga Shugaba Tinubu da ya cire Sarkin da ya naɗa ya ajiye a maƙabarta,” yana nuni da fadar Nasarawa da ake amfani da ita wajen binne Sarakunan Kano da suka riga mu gidan gaskiya.
Gwarzo ya soki yadda jami’an tsaro ke ci gaba da sintiri a fadar da wasu sassan birnin Kano, yana zargin su da harba hayaki mai sa hawaye da harsasai a kan masu zanga-zanga cikin lumana.
Ya jaddada cewa ba za su yarda da wata barazana ba, domin Kano tana da Sarki ɗaya tilo, kuma shi ne Muhammadu Sanusi II. Ya ce gwamnatin Kano za ta ci gaba da kare doka da oda tare da tabbatar da an mutunta hukuncin shari’a da ya mayar da Sanusi II kan karagar mulki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp