Gwamnatin Tarayya ta kalubalanci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023 da ya wuce, da ya rungumi salon yakin neman zabe na amfani da batutuwan kawo ci gaba, maimakon amfani da addini da kabilanci kamar yadda ya yi a zaben da ya wuce.
Gwamnatin ta ce babu abin da ya fi dacewa da mutum irin sa face ya nemi sana’a, domin siyasa ba irin ta shi ba ce.
- Za Mu Yi Wa ‘Yan TikTok Auren Gata – Hisba
- Kalaman Amurka Zai Iya Shafar Tattalin Arzikin Nijeriya – Minista
Ta ce ta rasa yadda Peter Obi wanda ta kira mai kwaikwayon abin da ya ga wani ya yi, da jam’iyyarsa ta LP suka hakikancewa kansu cewa su ne suka ci zaben da za a zahiri ya zo na uku.
Gwamnatin na mayar da martani ne ga wani taron manema labarai da Peter Obi ya gudanar a ranar Litinin, inda ta zarge shi da zubar da mutuncin bangaren shari’a.
Obi ya ce kotun koli ta yi watsi da shaida ta yankan shakku, kamar kin amfani da dokokin zabe da ya ce INEC ta yi, kuma abu ne da ya ce bai kamata hukumar zaben ta yi wasa da shi ba.
Sai dai gwamnatin ta ce dan takarar na jam’iyyar LP a zaben da ya wuce, yayin taron manema labaran da ya gudanar, tamkar Atiku Abubakar, ya yi kokarin zubar da mutuncin Kotun Koli da hukumar INEC saboda a cewarta, don kawai ba su ayyana shi wanda ya ci zaben 25 ga watan Fabrairu ba.
Ta ce kamata ya yi a zurfafa nazari kan babban mafarkin Peter Obi, wanda ya yi imanin cewa zai iya cin zabe ta hanyar gudanar da yakin neman zabe mafi haddasa gaba da janyo rarrabuwar kawuna da ya gwara kan Kiristoci da Musulmai da kuma wannan kabila da wata a kasa mai yawan kabilu da yawan addinai kamar Nijeriya.
Sanarwar da Babban Mashawarcin Tinubu kan harkar yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce Peter Obi ya yi kokari ba tare da nasara ba wajen tunzura ‘yan Nijeriya da karairayi da gugar zana, sannan ta zarge shi da yin tufka da warwara.
Gwamnatin Tinubu ta ce Obi ya amfana da hukunce-hukuncen kotuna a baya amma a yanzu yana bata sunan kotun saboda hukuncinta bai yi masa dadi ba.