Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya shawarci shugaba Bola Tinubu da ya kori duk wanda ya gaza aiki tukuru a gwamnatinsa.
El-Rufai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Maiduguri a ranar Litinin, inda ya yi kira ga shugaban kasa da ya yi abin da ya dace wajen cimma manufofinsa.
- Gwamnatin Katsina Ta Raba Wa Jami’an Tsaro Sabbin Motocin Yaki
- Majalisar Dokokin Kebbi Ta Dakatar Da Dan Majalisa Mai Wakiltar Birnin Kebbi Ta Arewa
“Ka bai wa mutum matsayi kuma ba ya aiki kamar yadda ka yi tsammani, ya kamata ka tsige shi, ka yi wani abu daban,” in ji El-Rufai.
El-Rufai ya kuma yi kira da ‘yan Nijeriya su yi addu’o’i sannan su mara wa gwamnati mai ci baya domin daidaita al’amura a kasar nan.
“Abin da ya kamata mu yi a matsayinmu na ’yan kasa shi ne mu yi wa shugabanninmu addu’a don Allah Ya yi musu jagoranci don su yi abin da ya dace.
“Domin Allah Ya ba su damar yin abin da ya dace; haka al’umma ke ci gaba,” in ji shi.