Tsohon shugaban kasan Nijeriya, Goodluck Jonathan ya jaddada cewa kabilanci da kurakuren zabe babba illace ga sha’anin shugabanci a daukacin Nahiyar Afirka.
Jonathan ya bayyana hakan ne da yake jawabi wurin taron taya tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo murnar cika shekara 87 a Abeakuta, ya zayyano abubuwan da ake bukata domin samun nagartaccen shugabancin al’umma.
- Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Da Su Tallafawa Matakan Siyasa A Sudan
- Ba Na Neman Zama Shugaban Kasa Ko Ta Halin Kaka – Peter Obi
Jonathan, wanda shi ne shugaban wannan taro, ya bayyana muhimman abubuwan da ake bukata a siyasa da shugabancin daukacin al’umma ba wai jam’iyyar siyasa ba kadai ba.
Ya bayyana adalci da iangantaccen siyasa a matsayin muhimman abubuwa da ke tabbatar da shugabanci nagari.
Tsohon shugaban kasan ya ce a duk lokacin da shugaba ya kasa hada kai da ‘yan adawa a gwamnatinsa, to zai rasa samun ingantaccen shugabanci. Ya siffanta wadanda suka yi nasarar cin zabe a siyasar Afirka a matsayin babban kalubale.